Zaɓen Amurka: Abin da Obama ya ce bayan nasarar Trump

Daga BELLO A. BABAJI

Tsohon shugaban ƙasar Amurka, Barack Obama ya taya zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Donald Trump murna bisa nasarar da ya samu.

Obama da matarsa, Michelle cikin wani saƙon gamayya, sun ce lallai ba su yi tsammanin haka sakamakon zaɓen zai kasance ba la’akari da rashin jituwa da ke tsakanin su da jam’iyyar Republican.

“Amma kasancewar a tsarin demokraɗiyya ake rayuwa wanda ba a kodayaushe ra’ayinmu ne zai yi nasara ba, ya sa mu karɓar miƙa mulki cikin salama.”

Amurka ta kasance ƙasa ce wadda a ƴan shekarun nan ake samun sauye-sauye musamman a ɓangaren hauhawar farashin kayayyaki da wasu annoba da ke faruwa a ƙasar, a cewar tsohon shugaban ƙasar.

Obama ya kuma ce, ci-gaba na da buƙatar miƙa wuya da dangana hatta ga waɗanda ake matuƙar adawa da su.

Gabannin zaɓen, Obama ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda ke fatan Kamala Harris ta jami’iyyar Democrat ta yi nasara tare da kushe Trump bisa tsare-tsarensa.