Zaɓen Anambra: Abin da ya sa INEC ta cire sunan Soludo daga jerin ‘yan takara

Daga WAKILINMU

Duk da yake tsohon gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Farfesa Charles Soludo, ya yi murnar cin zaɓen share fagen takarar gwamnan Jihar Anambra, murnar sa ta koma ciki domin kuwa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce ba ya cikin ‘yan takarar.

A jerin sunayen ‘yan takara da INEC ta fitar ranar Juma’a, sunan Chukwuma Michael Umeoji aka gani a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APGA, maimakon Soludo da ya shiga murna.

A jadawalin sunayen, hukumar ta rubuta kalmomin “umarnin kotu” a matsayin dalilin ta na sanya sunan Umeoji.

Haka kuma jam’iyyar PDP ba ta da ɗan takara a jerin sunayen da aka fitar saboda umarnin kotu kamar yadda jadawalin ya ce.

A cewar INEC, an tsara cewar za a gudanar da zaɓen gwamnan Jihar Anambra ne a ranar 6 ga Nuwamba, 2021.

Babban Kwamishina kuma shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Faɗakar da Masu Zaɓe na hukumar, Mista Festus Okoye, ya faɗa a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a cewa, “Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi taro a jiya Alhamis, 15 ga Yuli, 2021 kuma daga cikin abubuwan da ta tattauna, ta duba jerin sunaye da bayanan ‘yan takarar da jam’iyyun siyasa daban-daban su ka fitar don shiga zaɓen gwamnan Jihar Anambra wanda aka tsara za a gudanar a ranar 6 ga Nuwamba, 2021.

“Hukumar ta kuma duba tare da yin la’akari da hukunce-hukunce da umarnin kotu da aka kawo mata dangane da zaɓuɓɓukan share fage na jam’iyyun siyasa da sauran abubuwan da aka yi kafin zaɓen.

“Bisa ga tanadin da sashe na 31(3) na Dokar Zaɓe ta 2010 (wadda aka gyara) ya yi, za a wallafa bayanan rayuwar ‘yan takarar a allon sanarwar hukumar da ke Awka, a Jihar Anambra, yayin da kuma sunayen ‘yan takarar da jinsin su da jam’iyyar su da cancantar su, da kuma matsayi da kalaman hukumar ga su a nan an maƙala su. 

“Hukumar za ta ci gaba da yin aiki da Kundin Tsarin Mulki da doka kuma za ta ci gaba da bin hukunce-hukunce da umarnin kotuna da aka kawo mata.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *