Zaɓen APC: Wakilai 2,340 ne za su tantance ’yan takarar shugaban ƙasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A yau litinin ne jam’iyyar APC za ta gudanar da babban taronta a filin taro na Eagle Square da ke Abuja domin fitar da ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2023 mai zuwa.

Ziyarar da wakilin jaridar Blueprint ya kai wurin taron ya nuna cewa, jam’iyyar a shirye ta ke domin gudanar da wannan zaɓe wanda da yawa suka yi imanin cewa babu wani abin da zai iya hana wannan taro kasance ko kuma taɓarɓare taron.

Baya ga aikin tabbatar da tsaro, an riga an yi ado a wurin da kuma ware wa wakilan jihohi daban-daban wureren zama, da saka alluna da tutoci na masu neman shugabancin ƙasar daban-daban.

Zaɓaɓɓun wakilai 2,340 ne ake sa ran za su kaɗa ƙuri’a tare da zaɓen ɗaya daga cikin sama da mutane 23 da ke neman tikitin tsayawa takara.

Manyan ’yan takarar shugaban ƙasa, kamar yadda rahotannin tantancewar jam’iyyar APC suka nuna, sun haɗa da mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo, tsohon gwamnan jihar Legas, Ahmed Bola Tinubu, gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi da sauran mutane tara.

A lokacin da ya ke ƙaddamar da shugabanni da sakatarorin kwamitocin babban taro daban-daban a ranar Lahadi a sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa, shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana taron a matsayin babban taro da babu kamarsa.