Zaɓen cike giɓi: NNPP ta lallasa APC a Fagge

Daga BASHIR ISAH

Ɗan takarar Jam’iyyar NNPP, Barista MB. Shehu, ya lashe zaɓen ɗan Majalisar Wakilai na ƙaramar hukumar Fagge a Jihar Kano.

Nasarar da MB Shehu ya samu ta kawo ƙarshen ɗan majalisa mai wakiltar shiyyar a Majalisar Wakilai, Aminu Sulaiman Goro na Jam’iyyar APC wanda ke kan wa’adinsa na uku a Majalisar.

Da yake bayyana sakamakon zaɓen, Baturen zaɓen Ibrahim Tajo Suraj, ya ce MB Shehu ya samu ƙuri’u 19,024 daga jimillar ƙuri’un da aka kaɗa, yayin da ɗan takarar Jam’iyyar Labour, Shuaibu Abubakar ya rufa masa baya da ƙuri’u 12,789.

Sakamakon zaɓen ya nuna Aminu Sulaiman Goro na APC, shi ne ya zo na uku da ƙiri’u 8,669.

“Bayan cika duka sharuɗɗan da doka ta tanadar da kuma samun ƙuri’u mafi rinjaye, Barrister MB. Shehu na NNPP ne ya lashe zaɓe,” in ji Baturen Zaɓen.

Bayanan INEC sun nuna jimillar masu zaɓe 274, 031 aka yi wa rijista a yankin, sannan an tantance mutum 50, 852 yayin zaɓen.

Bayan kammalawa, ga yadda sakamakon zaɓen ya kasance:

APC – 8, 662
NNPP – 19, 024
PDP – 6, 548
LP – 12, 789