Zaɓen fidda gwani a APC: Buhari ya roƙi ‘yan jam’iyya su zama masu haɗin kai

Daga AMINA YUSUF ALI

A yayin da jam’iyyar APC take cigaba da zaɓen fidda gwani na takarar shugabancin ƙasar nan, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan jam’iyya da kuma daliget. Inda ya roƙi ‘yan Jam’iyyar APC da su kasance masu haɗin kai, su kuma daliget ya roƙe su a kan su tabbatar da sun zaɓo ɗan takara wanda zai ba wa jam’iyya dama ta kai bantenta a babban zaɓe.

Muhammadu Buhari ya bayyana haka a jawabinsa a safiyar yau Laraba a Abuja, a yayin da zaɓen fidda gwani na ‘yan takarar shugabancin ƙasar Nijeriya a jam’iyyar APC yake cigaba da gudana a dandalin Eagle Square.

Buhari ya ƙara da cewa, Yana roƙon ‘yan Jam’iyyar da su guji tashin hankali da junansu, sanan daliget su tabbatar ba su yi wa jam’iyyar zaɓen tumun dare ba, su zaɓi wanda aka san ba zai kunyata jam’iyyar ba a babban zaɓe mai zuwa na 2023.

A dai cikin jawabin nasa, Buhari ya bayyana cewa, babban ƙalubalen da yake gaban shugabancin jam’iyyar a ƙarƙashin Abdullahi Adamu shi ne, tabbatar da haɗin kan mambobin jam’iyyar don su cigaba da sadaukar da muradanmu saboda cigaban jam’iyyar.

Da ma dai tun kafin a fara zaɓen fidda gwanin shugaban ƙasar ya nemi shugabannin jam’iyya da daliget-daliget da su zama masu bin ƙa’ida da dokokin da suka shafi jam’iyyar wajen zaɓen gwanin da zai wakilci jam’iyyar a babban zaɓen 2023.

Sannan ya ƙara da cewa, dole ɗan takarar ya kasance mai ilimi, ɗan ƙasa na gari adali, kuma mai tsananin ra’ayin don haɗin kan ‘yan ƙasa, da kuma kyakkyawar nagarta da muradin ciyar da ƙasar nan gaba.

“‘Yan uwana ‘yan jam’iyya, kuma ‘yan ƙasa nagari, ina yaba muku a kan irin rawar da kuka taka da kuma gudunmowoyin da kuka bayar na samun nasarar gudanar da zaɓukan fidda gwani na jam’iyyar a fadin ƙasar nan. Ina yabawa ga masu ruwa da tsaki a jam’iyya, da shugabanni jam’iyya, da kuma kwamitin gudanar da jam’iyyar (NWC) jam’iyyar na ƙasa ƙarƙashin jagorancin Abdullahi Adamu”.

Daga nan shugaban ya taya murna ga waɗanda Allah ya ba wa nasara a zaɓukan fidda gwanin jam’iyyar, sanann ya yi kira ga waɗanda suka rasa takarar da su zama masu haƙuri da dangana.

Don a cewar sa da ma, duk inda aka yi takara dole a samu mai nasara da wanda ya faɗi. Don haka a cewar sa, da waɗanda suka yi nasara da waɗanda suka faɗin ya kamata su kawar da rashin fahimtar tsakaninsu, su rungumi jam’iyar su cigaba da taimaka mata kamar yadda suke yi a baya.