Zaɓen fidda gwani: Tinubu ya ziyarci Gwamna Bello don neman goyon bayan deleget

Daga BASHIR ISAH

Tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma ɗan takarar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ziyarci Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, domin neman goyon bayan deleget na jihar yayin zaɓen fidda gwani na APC mai zuwa.

Yayin ziyarar tasa a rana Juma’a, Tinubu ya gana da Gwamna Bello tare da ‘yan majalisarsa inda suka tattauna muhimman batutuwa.

Gwamna Bello tare da muƙarrabansa ne suka tarbi Tinubu da tawagarsa a filin jirgin saman da ke Minna Babban Birnin Jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *