Zaɓen fidda gwanin PDP: Tambuwal ya janye wa Atiku

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Sakkwato kuma ɗan takarar Shugaban Kasa a ƙarƙashin Jayyar PDP, Aminu Tambuwal, ya bayyana janyewarsa daga takarar shugabancin Nijeriya.

Tambuwal ya bayyana janyewar tasa ne sa”ilin da yake bayani wajen taron zaɓen fidda gwani na Jam’iyyar PDP ranar Asabar a Abuja.

Tambuwal ya bayyana dalilin janyewarsa da cewa, “Lokaci ya zo da za mu nuna sadaukarwa don cigaban jam’iyyarmu da kasarmu. Don haka, na yanke shawarar janye takararta.”

Bayan ɗaukar matakin janyewar, Tambuwal ya buƙaci duka daliget da ma magoya bayansa a haɗu a mara wa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *