Zaɓen Gwamna: Lawal ya kwaɓe Matawalle a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Da safiyar Talata Hukumar Zaɓe (INEC), ta bayyana Dr Dauda Lawal-Dare na Jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna a Jihar Zamfara.

Baturen zaɓen, Farfesa Kassimu Shehu da ya kasance Mataimakin Shugaban Jami’ar Tarayya da ke Birnin Kebbi, shi ne ya sanar da sakamakon zaɓen.

Ya ce Lawal-Dare ya lashe zaɓen ne bayan da ya samu ƙuri’u 377,726 daga ƙananan hukumomi 14 a jihar.

Wanda hakan ya ba shi famar kwaɓe gwamna mai ci, Bello Matawalle na Jam’iyyar APC daga kujerar Gwamnan jihar.

Matawalle ya tsira ne da ƙuri’u 311,976.