Zaɓen Gwamnoni: Gwamna Makinde ya kai bantensa

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar ƙarƙashin Jam’iyyar PDP.

Makinde ya lashe zaɓen ne da ƙuri’u 563,617 yayin da Sanata Teslim Folarin na APC ya rufa masa baya da ƙuri’u 251,230, sannan Adebayo Adelabu na jam’iyyar of the Accord ya zo na uku inda ya tsira da ƙuri’u 38,757.

A ranar Asabar aka gudanar da zaɓen gwamna a jihohi 28 daga cikin 36 da ƙasar ke da su.

Jihohi takwas ɗin da ba a yi zaɓen gwamna a cikinsu ba sun haɗa da Anambra, Bayelsa, Edo, Ekiti, Imo, Kogi, Osun da kuma Ondo wanda sukan gudanar da nasu zaɓen a lokaci mabambanta saboda dalili na shari’a da ya gitta.