Zaɓen gwamnoni: Kowa ya shiga tetayinsa, gargaɗin ‘yan sandan Kano ga masu shirin tada tarzoma

Daga RABIU SANUSI a Kano

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta gargaɗi duk wasu dake da niyyar haifar tashin hankali a zaɓen gwamnoni da majalisar jihar da za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, SP Haruna Abdullahi Kiyawa ya fitar a ranar Lahadi.

Jami’in ya ce dangane da bayanai da rundunar ke samu na ɗaura ɗamarar da wasu shugabanin siyasar suke yi na yunƙurin yin ta’ammali da ‘yan dabar siyasa don tayar da tarzoma yayin zaɓe mai zuwa a jihar.

Sanarwar ta ce, “kamar yadda Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Mamman Dauda, yake samun bayanai dangane da shirin da wasu baragurbin ‘yan siyasa suke yunƙurin yin amfani da ‘yan daba ranar zaɓen gwamnoni don haddasa husuma, ya gargaɗe su da su janye wannan ƙuduri na su, domin rundunar ba za ta ɗauki wannan rainin ba, za ta hukunta duk wanda aka samu da hannu ciki.

“Rundunar za ta ci gaba da haɗaka da sauran jami’an tsaro kowane ɓangare wajen ganin an kama duk wanda aka samu cikin laifin tare da gurfanar da shi gaban kotu don fuskantar hukuncin da ya dace.”

Kazalika, sanarwar ta ce Rundunar ‘yan sandan jihar na amfani da wannan dama wajen isar da saƙon godiya ga al’ummar jihar Kano bisa haɗin kai da goyon bayan da take samu musamman yadda aka gudanar da zaɓen Shugaban Ƙasa da Majalisun Tarayya.

Daga ƙarshe, Kwamishinan ya kuma ƙara miƙa saƙon buƙatar ‘yan jihar su ci gaba da ba da gudunmawarsa wajen wanzar da zaman lafiya jihar baki ɗaya.