Zaɓen Gwamnoni: Na yaba da aikin BVAS – Shugaban NITDA

Daga ABUBAKAR M. TAHIR

Shugaban Hukumar Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA), Kashifu Inuwa Abdullahi CCIE, ya bayyana gamsuwarsa kan yadda zaɓen gwamnoni yake cigaba da gudana a faɗin ƙasar nan.

Khashifu Inuwa ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan da ya kaɗa ƙuriarsa a akwati mai lamba 004 dake ‘Yan Dutsina, a mazaɓar Kasuwar Ƙofa dake Hadejia, Jihar Jigawa.

Ya ce, “Haƙiƙa na yaba da aikin BVAS mai tantance masu zaɓe, inda cikin ƙasa da daƙiƙa talatin ta yi aikinta jami’an zaɓe suka tantance ni na karɓi katin zaɓena”.

Ya ƙara da cewa, kowa ya yi zaɓe ya koma gefe ya jira sakamako ya bar wa Allah komai.

Ya ce haƙƙi ne a kan jama’a waɗanda shekarun suka kai su fito su zaɓi wanda suke so, kana a bi zaɓen da addu’a Allah ya ba wa wanda ya fi cancanta.

Daga bisani, Inuwa ya hori al’umma da su zama masu karɓar sakamakon zaɓe ba tare da tada tarzoma ba.