Zaɓen gwamnoni: Sarkin Keffi ya yaba da isowar kayan zaɓe a kan kari

Daga BASHIR ISAH

Mai Martaba Sarkin Keffi, Dr Shehu Chindo Yamusa II, ya yaba da yadda tsarin zaɓen wannan karon ya kankama a kan kari.

Basaraken ya nuna gamsuwarsa da yadda kayan zaɓen suka iso da wuri aka kuma tantance masu zaɓe a kan kari a zaɓen gwamnoni da majalisun jihohi a ranar Asabar.

Sarkin ya bayyana gamsuwarsa ne yayin da yake zantawa da manema labarai a fadarsa jim kaɗan bayna kaɗa ƙuri’arsa a rumfar zaɓe mai lamba 009, Tudun Ƙofa Ward da ke Ƙaramar Hukumar Keffi, Jihar Nasarawa.

Ya kaɗa ƙuri’ar tasa ce da misalin ƙarfe 8:42am, tare da yaba wa Hukumar Zave, INEC, kan yadda tsarin zaɓen ke gudana babu hayaniya.

“Addu’ata, yadda zaɓen ke gudana cikin lumana, Allah Ya sa a kammala shi cikin nasara,” in ji Sarkin.