Zaɓen gwamnoni: Shugaban Ƙasa mai jiran gado ya kaɗa ƙuri’arsa

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa mai jiran gado, Bola Tinubu, ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen gwamnoni da na majalisun jihohi da ke gudana a wannan Asabar.

Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, ya rawaito cewar Tinubu ya kaɗa ƙuri’arsa ne da misalin ƙarfe 9:35 na safe a Rumfar Zaɓe 085 a Gunduma 03, da ke Alausa, Ikeja, Jihar Legas.

Bayanai sun ce ya yi zaɓen nasa ne cikin yanayi mai tsatssauran tsaro.

Matarsa, Oluremi da Sarkin Kasuwa Legas, Cif Folashade Ojo, na daga cikin waɗanda suka take wa Tinubu baya zuwa rumfar zaɓe.