Zaɓen Kaduna: PDP ta lashe mazaɓar El-Rufai

Jam’iyyar PDP ta lashe mazaɓar Gwamna Nasir El-Rufai ta Unguwar Sarki a zaɓen ƙananan hukumomi da ya guda a jihar jiya Asabar.

Sakamakon zaɓen ya nuna ‘yan takarar PDP, na ciyaman da kansila, su ne suka samu ƙuri’u mafi yawa a mazaɓar gwamnan.

Tun farko Gwamna El-Rufai, wanda ɗan jam’iyyar APC ne, ya kaɗa ƙuri’arsa a mazaɓarsa da ke Unguwar Sarki cikin Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa, inda a nan ya nuna cewa shi ba ya da niyar sai ya yi nasara ko ta halin ƙaƙa, amma yana fatan ganin yanayin zaɓen ya inganta.

Gwamnan ya ce salon amfani da na’ura wajen kaɗa ƙuri’a da gwamnatinsa ta zo da shi, hakan ya nuna ƙarara cewa gwamnatin jihar Kaduna ƙarƙashin jam’iyar APC ba ta yarda da maguɗin zaɓe ba.

Sa’ilin da yake bayyana sakamakon zaɓen, jami’in zaɓe mai kula da mazaɓar El-Rufai, Muhammad Sani, ya ce ƙuri’u 62 yayin da PDP ta samu 86 daga cikin jimillar ƙuri’u 159 da aka kaɗa ga masu neman shugabancin ƙaramar hukuma.

A ɓangaren kansiloli kuwa, baki ɗaya ƙuri’u162 aka kaɗa, daga ciki APC ta samu 53 sannan PDP ta tashi da ƙuri’u 100.

Kodayake dai ya zuwa haɗa wannan labari ba a kai ga bayyana baki ɗaya sakamakon zaɓen ƙaramar hukumar Kaduna ta Arewa ba, sakamakon ana jiran isowar sauran sakamako daga sassan ƙaramar hukumar.