Zaɓen Kano: Abba ya sake tsere wa Gawuna a yawan ƙuri’u

Daga WAKILINMU

A ci gaba da rigegeniyar da ake yi tsakanin jam’iyyun APC da NNPP wajen lashe zaɓen Gwamnan Jihar Kano, yanzu haka NNPP ta sake tsere wa APC a yawan ƙuri’u.

Bayan tattara sakamakon zaɓe na ƙananan hukumomi 30, Abba Bichi Yusuf na NNPP ya samu ƙuri’u 567,135 yayin da Nasir Gawuna na APC ke da ƙuri’u 567,352, wato bambanci ƙuri’u 217 ke tsakani a halin yanzu.