Zaɓen Katsina: Dikko Raɗɗa ya tsere wa Lado Ɗanmarke a yawan ƙuri’u

Daga UMAR GARBA a Katsina

Zuwa yanzu hukumar zaɓe mai zaman kanta a jihar Katsina ta tattara sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi 21 cikin 34 da ake da su a jihar inda ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Dikko Raɗɗa, ya tsere wa abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, wato Yakubu Lado Ɗanmarke a yawan ƙuri’u.

Ga sakamakon zaɓen kamar yadda Baturen zaɓen, Farfesa Yahaya Maƙarfi ya bayyana a ɗakin tattara sakamakon zaɓen:

  1. Ƙaramar hukumar Sandamu
    APC – 21,055
    PDP – 10,641
    NNPP- 01
    PRP – 03
  2. Ƙaramar Hukumar Ɓaure
    APC – 32,802
    PDP – 17,888
    NNPP- 62
    PRP – 12
  3. Ƙaramar Hukumar Dutsi
    APC – 15,631
    PDP – 8,419
    NNPP- 10
    PRP – 10
  4. Ƙaramar Hukumar Batagarawa
    APC – 26,326
    PDP – 13,510
    NNPP- 212
    PRP – 81
  5. Ƙaramar Hukumar Ingawa
    APC – 22,080
    PDP – 12,255
    NNPP- 209
    PRP – 217
  6. Ƙaramar Hukumar Bindawa
    APC – 28,997
    PDP – 12,165
    NNPP- 957
    PRP – 47
  7. Ƙaramar Hukumar Kaita
    APC – 24,121
    PDP – 9,824
    NNPP- 53
    PRP – 20
  8. Ƙaramar Hukumar Mai’Adua
    APC – 28,436
    PDP – 11,506
    NNPP- 68
    PRP – 10
  9. Ƙaramar Hukumar Ɗandume
    APC – 23,710
    PDP – 14,792
    NNPP- 220
    PRP – 146
  10. Ƙaramar Hukumar Mani
    APC – 29,678
    PDP – 16,180
    LP- 16
    NNPP- 231
    PRP: 28
    SDP – 10
  11. Ƙaramar Hukumar Kusada
    APC – 13,750
    PDP – 11,151
    LP- 04
    NNPP- 05
    PRP: 17
  12. Ƙaramar Hukumar Rimi
    APC – 28,202
    PDP – 13,823
    LP- 13
    NNPP- 397
  13. Ƙaramar Hukumar Zango
    APC – 19,757
    PDP – 10,477
    NNPP- 04
    PRP – 14
  14. Ƙaramar Hukumar Safana
    APC – 15,417
    PDP – 10,450
    LP- 02
    NNPP- 09
    PRP: 53
    SDP – 143
  15. Ƙaramar Hukumar Funtua
    APC – 31,924
    PDP – 19,849
    LP- 39
    NNPP- 314
    PRP: 218
    SDP – 03
  16. Ƙaramar Hukumar Daura
    APC – 26,548
    PDP – 10,689
    LP- 08
    NNPP- 78
    PRP: 27
    SDP – 08
  17. Ƙaramar Hukumar Mashi
    APC – 28,793
    PDP – 8896
    LP- 08
    NNPP- 74
    PRP: 11
    SDP – 102
  18. Ƙaramar Hukumar Batsari
    APC – 20,053
    PDP – 10,247
    LP- 11
    NNPP- 239
    PRP: 158
    SDP – 02
  19. Ƙaramar Hukumar Jibiya
    APC – 21,216
    PDP – 13,259
    LP- 08
    NNPP- 22
    PRP: 34
    SDP – 05
  20. Ƙaramar Hukumar Musawa
    APC – 24,632
    PDP – 10,118
    NNPP – 580
  21. Ƙaramar Hukumar Sandamu
    APC – 21,055
    PDP – 10,641
    NNPP – 01

‘Yan takara 13 ne ke fafatawa a zaɓen sai dai takarar tafi zafi tsakanin ɗan takarar jam’iyyar APC Dikko Umar Raɗɗa da takwaransa na PDP, Sanata Garba Yakubu Lado Ɗanmarke.