Zaɓen mace ko namijin aure (IV)

Assalam alaikum. Ina godiya ga Allah da ya sa ke ba ni damar rubuta wasiƙa zuwa ga ’yan uwana matasa a wannan jarida mai albarka ta Blueprint Manhaja.

Wasu malamai sun kawo shi kamar haka:

1- Ya san cewa istimna’i yana daga zunubai da aka yi alƙawari azaba ga mai yinsa.

2- Ya san cewa mutane za su ƙyamace shi idan suka san yana yinsa.

3- Ya taimakawa kansa da yin azumi domin dawo da ƙarfin iradarsa.

4- Ya shagaltu da muɗali’ar littattafai, da nau’o’in irin wasanni kamar wasan gudu da tseran doki da sauransu.

5- Iyaye su kula da tarbiyyar ’ya’yansu tun farkon rayuwarsa, ta yanda zasu kula da dukkan halayensa domin gyara da ba shi tarbiyya ta gari.

6- Dole ne al’umma da hukuma su bayar da muhimmanci na musamman kan sha’anin aure.

7- Mai wannan halin ya duba irin bala’in da ya ke faɗa masa na cututtukan ruhi da na jiki, kamar cututtukan fata, rashin jin cikakken daɗin kusantar mace, rashin matsayi a al’umma saboda matsalar jijiyoyi da gajiyawar jiki, da sauransu.

Mu sani yawan duba littattafan hikima da na ilimi , da yawan tafiye-tafiye , da wasannin motsa jiki , da koyon harbe-harbe, da koyon sukuwar doki, da iyo a ruwa, suna daga cikin abubuwan da suke ƙarfafa ruhin mutum , kuma suna kawo lafiyar jiki da ta ruhi da nishaɗi ga rayuwar mutum, kamar yadda suna kawo farin ciki da annashuwa.

Daga cikin shawarwari da aka bayar ga mai yawan sha’awar da ta fita daga al’ada, musamman Waɗanda sha’awarsu ta kai su ga lalacewa da babu wani haramun da ba zasu iya bari ba ta hanyar biyan buqatarsu ta haram, sun haɗa da:

1- Tunawa da munin wannan hali, da abin da ya ke haifarwa na cututtukan ruhi da jiki, da jawo wa mai wannan hali saurin tsufa da mutuwa a rayuwarsa ta duniya.

2- Karya ƙarfin sha’awarsa da yawaita yin azumi, da zama da yunwa, da ƙaranta cin abinci.

3- Ƙoƙarin ganin ya yi maganin duk wata hanya da takan iya kai shi ga jin sha’awa, kamar; tunanin abubuwan da sukan jawo masa sha’awa, da magana da mata, da kallon mata, da keɓewa da mace, da kallon fina-finan banza da dukkan wani abu da zai iya sanya shi jin sha’awa.

4- Yin amfani da hanyoyin da za su hana shi aikta haram da sha’awarsa kamar gaggauta yin aure da zaran ya samu dama; auren na da’imi ne ko kuma na mutu’a.

5- Tuna ni’imar da Allah ya ke bayar wa ga wanda ya bar sha’awarsa ya qi aikata haramun da ita, saboda Allah.

6- Sanin cewa wannan siffa ce ta dabbobi, shi kuwa mutum ne bai kamata ba ya zama kamar dabba domin shi an halicce shi ne domin kamala.

7- Ya yi duba da tunani da lura zuwa ga ayoyin Ƙur’ani da ruwayoyi da su ka kwaɗaitar da tuba, suka kuma zargi mai wannan hali.

8- Ya yawaita karatun Ƙur’ani da karanta littattafai na ilimi na hikima, da yawaita addu’a, da jin cewa shi zai iya barin wannan hali, haɗa da matakan da muka ambata a sama.
Wassalam.

Wasiƙa daga Mustapha Musa Muhammad, ɗalibi a fannin karatun Injiniyancin Sinadarai (Chemical Engineering) a Jami’ar Federal Polytechnic Kaduna, 09123302968.