Zaɓen Nasarawa: A.A Sule ya zarce

Daga BASHIR ISAH

Ya tabbata Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa zai mulki jihar a wa’adi na biyu.

A wannan Litinin Hukumar Zaɓe, INEC, ta ayyana Gwamna Sule a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar wanda ya gudana ranar Asabar.

Baturen zaɓen, Farfesa Tanko Ishaya, shi ne ya ayyana Abdullahi Sule na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri’u 347,209.

Inda ya doke ɗan takarar PDP, David Ombugadu, wanda ya samu ƙuri’u 283,016.

Sai dai jam’iyyar PDP a jihar ta nuna rashin gamsuwarta da sakamakon zaɓen, tana mai cewa za ta ƙalubalanci nasarar da A.A Sule ya samu a kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *