Zaɓen Ondo: Kotu ta yi watsi da ƙarar da PDP ta shigar

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta jihar Ondo, ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar PDP ta jihar da ɗan takararta Eyitayo Jegede, suka shigar inda suke ƙalubalantar nasarar da Gwamna Oluwarotimi Akeredolu SAN na APC ya samu a zaɓen gwamnan jihar da ya gudana ranar 10 ga Oktoban 2020.

Kotu ta kori ƙarar ne saboda rashin ƙarfin iko da cancanta.

Da yake gabatar da shari’ar ta bidiyo, shugaban kotun, Alƙali Umar Abubakar, ya ce batun da aka shigar da ƙara a kansa abu ne da jam’iyyar za ta sasanta ta cikin gida ba tare an kai kotu ba, wanda a cewarsa kotu ba ta da hurumin sauraron ƙarar.

Da wannan ne kotun ta yanke hukunci kan cewa nasarar da Akeredolu ya samu na nan daram.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *