Zaɓen Osun: Ta leƙo ta koma wa Adeleke

Daga WAKILINMU

Kotun Sauraron Kararrakin Zaɓe a Jihar Osun, ta tabbatar da Adegboyega Oyetola na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen Gwamna da aka gudanar a Jihar ran 16 ga Yulin bara.

Bayan kammala zaɓen, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta ayyana Ademola Adeleke na Jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen, lamarin da APC ta ce ba ta yarda da sakamakon zaben ba ta kuma shigar da ƙara.

Yayin da yake yanke hukunci, Alƙali Tetsea Kume, ya ce INEC ba ta yi amfanin da tsarin da Kundin Tsarin Mulki da Dokar Zaɓe suka shimfiɗa ba.

Kazalika, ya ware ƙuri’un da aka yi arigizonsu daga jimillar ƙuri’un da kowane ɗan takara ya samu kafin ayyana Oyetola a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri’u 314,921, yayin da Adeleke ya tashi da ƙuri’u 290,266.

Aƙalin ya umarci INEC da ta janye shaidar lashe zaɓen da ta bai wa Adeleke sannan ta miƙa sabuwar shaida ga Oyetola wanda ya lashe zaɓe a halasce.