Zaɓen Sanatan Kebbi ta Arewa bai kammala na – INEC

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Hukumar INEC ta ce za Kamar yadda bayanai suka zo daga hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kebbi ta an bayyana za a sake zabe a rumfuna 30 masu ƙuri’u 16,940.

Rumfanan zaɓen da lamarin ya shafa sun haɗa da:

Arewa rumfa 1, mai lamba 02
Argungu rumfa 2, mai lamba 03.
Augie rumfa 4, mai lamba 04.
Bagudo rumfa 4, mai lamba 05.
Dandi rumfa 7, mai lamba 08.
Suru rumfa 12, mai lamba 018.

Tazarar da ɗan takarar Sanata na PDP, Dr. Yahaya Abubakar Abdullahi Mallamawan Kabin Argungu ya bai wa takwaransa na APC, Dr. Hussaini Suleiman Zango Kangiwa Sarkin Arawan Kabin Argungu ta kai kimanin ƙuri’a 8606.

Za a sake zaɓen ne sanadiyyar samun ƙuri’u fiye da mutanen da aka tantance yayin da waɗansu rumfuna kuma aka sami hatsaniya tsakanin magoyabayan jam’iyyu.

Hukumar dai ta sanar da cewa za a sake zaɓen ne mai yiyuwa wani sati kafin na gwamnoni da ‘yan majalisun dokoki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *