Zaɓen Shugaban Ƙasa bai cimma muradin ‘yan Nijeriya ba – Amurka

Daga BASHIR ISAH

Mako guda bayan gudanar da zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘yan majalisun tatayya a Nijeriya, ƙasar Amurka ta ce zaɓen bai cimma muradun ‘yan ƙasar ba.

Cikin sanarwar da ta fitar ranar Lahadi, Jakadiyar Amurka a Nijeriya, Mary Beth Leonard, ta ce, da yawan ‘yan Nijeriya ransu a ɓace yake game sa zaɓen yayin da wasu su ke cikin murnar lashe zaɓe.

“A bayyane yake cewa baki ɗaya, zaɓen da ya gudana ran 25 ga Fabrairu bai cimma muradun ‘yan Nijeriya ba.

“‘Yan Nijeriya sun nuna ƙwazo yayin zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu wajen tabbatar da dimokuraɗiyya, sai dai akwai ‘yan ƙasar da dama da suka fusata da takaici da kuma wasu da dama da ke murnar nasarorin da suke ganin an samu.

“A gaba, zai yi kyautu ga makomar ƙasar kada ‘yan Nijeriya su bari su rarraba saboda bambancin da ke tsakani, sannan a riƙa amfani da hanyoyin da doka ta shimfiɗa wajen warware kowane irin ƙalubale,” in ji ta.

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ayyana Bola Tinubu na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen Shugaban Ƙasa da ƙuri’u 8,794,726, yayin da Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP ya rufa masa baya da ƙuri’u 6,984,520.

Kodayake Atiku da Obi, baki dayansu sun ce za su ƙalubalanci nasarar Tinubun a kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *