Zaɓen Shugaban Ƙasa: Jega da Mabari za su jagoranci tawagar ECOWAS zuwa Laberiya

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Ƙarfafa Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), ta tura tawagar haɗin gwiwa zuwa ƙasar Laberiya domin bincike kan shirye-shiryen da ƙasar ta yi gabanin gudanar da babban zaɓe a ƙasar.

Ya zuwa ranar 10 ga watan Oktoban 2023, Laberiya za ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar ƙasar.

Majiyarmu ta ce tawagar da ECOWAS ta tura ƙasar, za ta yi aikinta ne daga 23 zuwa 29 ga Yuli, kuma ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Hukumar Zaɓe ta Nijeriya (INEC), Farfesa Attahiru Jega da Ambasada Calixte Mbari jigo a ƙungiyar Ƙaɗin Kan Afirka (AU).

Sauran mambobin tawagar sun haɗa da: Ambasada Haja Alari Cole, Ms. Jean Mensa daga Ghana, Mr. Elyse Ouedraogo daga Burkina Faso, M. Muhammad Sulaiman Isa daga Nijeriya, Dr Cyriaque Agnekethom da sauransu.

Yayin ziyarar tata, ana sa ran tawagar za ta yi zama da masu ruwa da tsaki kan sha’anin zaɓen ƙasar, ciki har da gwamnatin ƙasar da hukumar zaɓe, fannin shari’a da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *