Zaɓen wannan karon ya ɗara wanda ya gabata inganci, in ji Sakkwatawa

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Yayin da harkokin zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi ke ci gaba da gudana, wasu ‘yan ƙasa sun bayyana ra’ayoyinsu game da zaɓen.

Ziyarar da wakilinmu ya kai a sassan birnin na Sakkwato, kusan bayanin duka ɗaya ne, inda masu jefa ƙuri’a suka nuna gamsuwarsu.

Daga cikin waɗanda wakilin namu ya zanta da su, sun bayyana cewa an samu sauyi a zaɓen wannan karon idan aka kwatanta da zaɓen Shugaban Ƙasa da ya gabata.

A cewarsu, ingancin zaɓen wannan karon ya ɗara na wanda ya gabata.