Zaɓar mace ko namijin aure (I)

Assalam. Ina godiya ga Allah da ya ba ni damar rubuta wannnan wasiƙa zuwa ga ’yan uwana matasa a wannan jarida mai albarka ta Blueprint Manhaja.

A Musulunci an yi umarni ne da a yi aure ba domin biyan buƙata ta duniya ko ta sha’awa ba kawai, akwai buƙata ta gina al’umma saliha da za ta ci gaba da ɗaukar nauyin isar da saƙon Allah a duk faɗin Duniya, wanda wannan yana buƙatar taimakekeniya tsakanin ma’aurata, sa’annan akwai samun nutsuwa ta ruhi da ɗan Adam yana buqatarsa wanda an sanya shi ne ya zamanto ta hanyar zamantakewa tsakanin miji da mata.

Misali mace koda ta yi ilimi kuma ta samu komai na wannan duniya, da dukkan ni’ima, haka nan ma namiji, idan ba su da mai ɗebe musu kewa ta fuskacin zaman auratayya to akwai wani giɓi babba da ba su cike shi ba, wanda ba ya samuwa sai ta hanyar auratayya, wacce Ƙur’ani mai girma ya yi nuni da ita , kamar yadda a zamantakewar tare tsakanin ma’aurata idan aka mayar da ƙauna da so suka koma ƙiyayya da gaba, abin yakan fi zama ba tare da mai ɗebe kewa ba muni.

Kamar yadda haka nan ana son yin aure da wuri ga wanda ya balaga matuƙar ya samu yalwa, domin a cikin rashin yin hakan akwai fitina a bayan ƙasa da fasadi mai girma kamar yadda ya zo daga Ahlul Baiti (A.S). Mu sani akwai kamalar da ba ta yiwuwa a san ta ko a kai zuwa gareta sai ta hanyar aure, kuma ba ta samuwa ta hanyar zaman banza da fasiƙanci. Irin waɗannan abubuwan sun haɗa da; sanin ma’anar ciyarwa, yafewa, soyayya, haƙuri, juriya, ɗaukar nauyin mutane, reno, tarbiyyar ’ya’ya, fahimtar ƙimar iyaye, tunanin gida da sauransu.

Ayatul-Lahi Makarim Shirazi yana cewa, sauda yawa daga cikin abubuwa kamar ma’anar soyayya, da ƙauna, da yafewa, da kyauta, da baiwa da tausayi, da fansar rai, ma’anarsu ba ta ganuwa da fahimtuwa sai da aure, wanda zaman banza ba tare da aure ba da matar haram ko zaman gwauranci da rashin aure ba za a iya fahimtar haƙiƙaninsu ba, kuma riskarsu tana yiwuwa ta hanyar zamantakewar aure ne kawai.

Masu ilimi sun kawo wasu abubuwa kamar haka da sukan kawo jinkirin aure:

1- Tsawon muddar lokacin karatu: ta yadda saurayi ko budurwa kafin ya kai ga kammala jami’a ya kai shekara talatin zuwa talatin da biyar a mafi yawan lokuta, sauda yawa wannan yakan jefa wasu cikin halin da suka katse karatu idan ba za su iya haɗa biyun ba, don haka yana kan al’umma da gwamnatocinsu su yi tunanin maganin wannan koda ta hanyar tallafi ne a kan ’yan makaranta. Misali a nan a ƙasar farisa sukan yi ƙoƙarin yi wa dubunnan ɗaliban jami’a aure a kyauta kowace shekara da kuma ba su tallafi.

2- Samun damar yin alaƙar Haram: Yawaitar gidajen karuwai da wajajen fasiƙanci sauda yawa yakan sanya wasu samari su ga ya fi musu sauƙi su je su yi mummunar mu’amala ta Haram da matan banza na wani ɗan lokaci tsawon rayuwar samartakarsu. Wannan ma wani abu ne da musulunci ya sanya mafita gare shi ta hanyoyi da dama kamar haka:
a- Tallafin aure da wuri daga Baitul Mali ga dukkan wanda ba zai iya aure ba kuma da buƙatar hakan domin ya balaga.
b- Tarbiyyantarwa ta hannun malamai, da kafafen watsa labaru da jaridu da makarantu.
c- Hana gidajen fasadi da kulle duk wani waje da ake ashararanci.
d- Wayar da kan mutane da ilimantar da su domin su san illar wannan mummunan hali da abin da ya ke jawowa.
e- Idan ma’abota wannan halin ba a shirye suke su yi aure ba koda kuwa suna da yalwa, to musulunci har yanzu ya ba su damar yin auren mutu’a, don haka ne ma idan irin waɗannan wajajen ba za su ƙullu ba, sai waɗannan mata masu zaman kansu su tuba daga wannan ayyuka, maimakon su riqa zina sai su yi auren Mutu’a da duk wanda suke so, bayan muddar ta ƙare sai su yi idda.

Wasu malamai suna ganin gwamnatin musulunci tana iya mayar da gidajen banza su koma gidajen shari’a ta wannan hanya, musamman gudun cewa irin waɗannan mutane idan aka kore su, to zasu koma suna fasiƙanci a voye, maimakon haka sai su tuba su bi hanyar da shari’a ta gindaya musu.

Za mu ci gaba a mako mai zuwa. Wassalam.

Daga Mustapha Musa Muhammad, ɗalibi a fannin karatun Injiniyancin Sinadarai (Chemical Engineering) a Jami’ar Federal Polytechnic Kaduna, 09123302968.