Zaɓe bayan cika shekaru 24 a wata mai zuwa

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Tun da a ka fara mulkin dimokraɗiyya a Nijeriya wanda ya samo asali daga samun ’yancin ƙasar a 1960 an samu mulkin farar hula a zaɓuka daban-daban inda gabanin zaɓen 1999 an samu shigowar sojoji ne da su ka kifar da gwamnatin farar hula.

A ranar 15 ga watan Janairun 1966 sojoji ’yan zubar da jini sun kifar da gwamnatin firaminista Sir Abubakar Tafawa Balewa wanda hakan ya jawo yankewar mulkin farar hula har sai a 1979 inda a ka gudanar da zave marigayi Shehu Shagari ya lashe a qarqashin jam’iyyar NPN mai alamar masara.

A lokacin da a ka dawo sabon zaɓe a 1983 sojoji sun kifar da gwamnatin inda shugabannan mai ci Muhammadu Buhari ya dare karaga cikin kakin soja kuma gwamnatin sa ta soke dukkan harkoki na farar hula da ma tsare kusan dukkan jagorin farar hulan na lokacin ciki har da zaɓaɓɓen shugaban Shagari. Haka sojojin su ka samu saɓani da juna su ka kifar da gwamnatin soja ta Buhari inda Janar Ibrahim Babangida ya zama shugaba kuma ya ƙirƙiro jam’iyyu biyu SDP da NRC inda a ka shirya zaɓe amma hakan bai kai ga miƙa mulki hannun farar hula ba.

Za a tuna zaɓen da a ke ta labari har yanzu na 12 ga watan Yuni 1993 wanda a ka ce marigayi Moshood Abiola ne ya lashe da mataimakinsa Babagana Kingibe. A zahiri tun lokacin da shugaban mulkin soja Janar Abdulsalami Abubakar ya mika ragama ga ɗan uwansa tsohon soja Janar Olusegun Obasanjo a 1999 a ka samu wanzuwar mulkin farar hula har bana a ke cika shekaru 24 cif.

Ko ma dai me za a ce jam’iyyu biyu ne su ka mamaye mulki a tsawon shekarun wato PDP da ta yi shekaru 16 inda ita kuma APC yanzu ta samu rabin shekarun wato shekaru 8 kuma ta ke fatan zarcewa kan mulki har illa Masha Allahu. An ga kamun ludayin jam’iyyar PDP da ta juye a ke ganin ta ta ’yan jari hujja ne zuwa gamaiyar ‘yan adawa da ta zama APC.

In ƙasar ta gyaru an sani in ma akasin hakan a ka samu duk dai ga mu nan dai mu na gani. Masu zaɓe ko da za a zargi wasun su da biyewa son zuciyar bambancin aƙida, yanki ko ƙabila, dai sun ba wa kowane kalar ɗan siyasa dama ya shiga fadar Aso Rock ya baje kolinsa da ƙarfin ikon shugaban Nijeriya da masu sharhi ke cewa kusan ba wanda ya fi shugaban Nijeriya ƙarfin tasirin mulki a duniya.

Da a ka zo fassara tsarin mulkin shugaban ƙasa mai cikekken iko saɓanin mai firaminista a Nijeriya sai a ka ambaci hakan da “MAI WUƘA DA NAMA” kun ga kuwa wanda a ka ba shi wuka da nama sai ya yanki gefen tsoka kuma ya reɗe kitse daga kashi ko ya zunuro bargo ya yi yadda ran sa ya ke so. Ita kan ta majalisa ba ta iya yi wa shugaban Nijeriya komai tun daga fara dimokraɗiyyar.

In za a duba ai an samu sauyin shugabannin Majalisar Dattawa da wakilai ta hanyar tsigewa amma hakan ko da wasa bai tava zuwa kan shugaban ƙasa ba kuma ba za a iya cewa shugabannin Nijeriya ba sa murƙushe doka da hakan zai iya kai wa ga imma su yi murabus ko a tsige su ba.

Shin dimokraɗiyyar Nijeriya ta biyawa ’yan Nijeriya buƙatun su ko da sauran tafiya? Har shekaru na wa za a kai a ce dimokraɗiyyar Nijeriya ta girma? Yo ko ma dai ba ta biyawa ‘yan Nijeriya buƙata ba, ta biyawa wasu ‘yan ƙalilan muardun su na rayuwar duniya sai dai a jira kiyama nan kuma sai abun da mutum ya aikata.

Ko dimkoraɗiyyar ba ta girma ba amma ta girmama wasu mutane ƙalilan da ke shawagi a jiragen sama da iyalin su ba sa bin tituna balle a sace su. Yanzu dai za mu ga aƙalla an samu fiye da jam’iyya ɗaya da ke da tasiri ko ba na lashe zaɓen shugaban ƙasa ba za ta iya tavukawa.

Ba mamaki a farkon dimokraɗiyyar da a ka samu jam’iyyu kusan uku da su ka samu kujerun gwamnonin jihohi da ma na majalisa don a lokacin a ka fara. A sannu-sannu sai ta kai ga in ba ɗan takara ya tsaya a inuwar PDP ba, ba zai lashe zaɓe ba a akasarin kujerun. Yanzu kuma ga APC nan ta maye gurbin PDP.

Ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare kuma in da ba kasa a ke gardamar kokawa. Ya zama wajibi masu zaɓe su ƙara dagewa wajen zabar abun da zai zama alheri ga kasar su ba ga kan su ko garin su ko ƙabilarsu ba. Duk ’yan takara sun wasa wuƙarsu ta lashe zaɓe don haka sai a yi fatar alheri cewa wanda ya lashe zaɓe na gaskiya shi za a aiyana a matsayin wanda ya samu nasara.

Masana na bayyana cewa sai ’yan Nijeriya a dukkan sassa sun yi zaɓe nagari ba da la’akari da wani bambanci ba ne za a iya samun cin gajiyar arzikin ƙasar mai yawa. Bayanan masanan da masu sharhi na zuwa ne gabanin babban zaɓen Nijeriya a ranar 25 ga watan gobe kamar yadda jadawalin hukumar zave ya tsara.

Masanan na cewa duk matsalolin ƙasar da su ka haɗa da na tsaro da ƙuncin tattalin arziki za su kawo ƙarshe idan masu zave su ka duba waɗanda su ka cancanta kama daga muƙaman zartarwa da na majalisa.

Masanin kimiyyar siyasa na jami’ar Abuja Dr.Abubakar Umar Kari ya ce kama daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa PDP da ke adawa ba sa marmarin duk sauye-sauye da a ka samu a dokar zave da za ta iya yi mu su barazanar samun nasara kamar yadda a ka faro tun 1999.

Shi ma masanin kimiyyar siyasa na jam’iar Bayero Dr.Sa’idu Ahmed Dukawa ya ce da zarar talakawa sun kauce wa son zuciya su ka samu dora jagorori nagari a zaven sun huta da ƙalubalen da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa na rashin tsaro, talauci, rashin magani a asibiti da sauran su.

Shugaban kwamitin amintattu na gamaiyar qungiyoyin Arewa Nastura Ashir Sharif ya ce duk matsalolin da ke addabar Nijeriya na bayan taɓarɓarewar tsaro da in an ɗauki matakan da su ka dace za a iya samun maslahar sauran matsalolin. Sharif ya ƙara da cewa zai yi tasiri a ɗauki jami’an tsaro ɗari biyar-biyar daga kowace ƙaramar hukuma don kula da sako da lunguna da hakan lalle zai kawo sauyi.

Mai sharhin kan lamuran yau da kullum ya nuna kyamar yadda ya ce gwamnatin shugaba Buhari ta ciwo bashin da ba taba samun irin hakan ba a tarihin Nijeriya hakanan kuma gwamnatin ta vullo da ba da haraji barkatai

A tabaron Dr.Kari gwamnoni sun mamaye ƙarfin wannan zaɓe na 2023 kusan fiye da kowane lokaci da har ƙungiyoyi su ke kafawa na cimma muradun su.

Wannan komawa dimokraɗiyya dai ita tafi jan zare da samun shekaru 24 in an ma kwantanta ta farko da ta yi shekaru 6 ta biyu ta yi 4 inda sojoji su ka kifar da gwamnatin Shagari. Babban hafsan rundunar sojan Nijeriya Lucky Irabor ya ce sojoji na mara baya 100% ga gwamnatin dimokraɗiyya.

Wannan na kwaranye barazanar juyin mulki da a ke fargaba matuqar ’yan siyasa su ka gaza haɗa kai. Masui ya magana na cewa sai bango ya tsage kadangare kan samu wajen shiga.

Shugaban hukumar zaɓen Nijeriya INEC a taƙaice Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana dalilan da su ka saka ’yan Nijeriya da ke ƙetare ba za su iya kaɗa ƙuri’a a zaɓen nan na 2023 ba mai zuwa a watan gobe.

Farfesa Yakubu na magana ne a jawabi da ya gabatar a CHATTAM HOUSE da ke London kan shirye-shiryen babban zaven.

Shugaban na INEC ya ce dokokin Nijeriya ne ba su amince wanda ba ya zaune a cikin ƙasar ya yi rejista ba balle har ya samu damar yin zaɓe.

Yakubu ya ce, hukumar na goyon bayan ‘yan Nijeriya da ke ƙetare su samu damar gudanar da zaɓen amma ya zama wajibi a mutunta tanadin dokokin ƙasa.

A nan Yakubu ya ce, lokaci zai kai ga samun damar waɗanda ke zaune a qetare su iya kaɗa ƙuri’a bayan an gyara doka da hakan zai ba da damar.

Kammalawa;

In dai har ƙuri’a za ta zama da gaske maƙamin talaka ne to ya na da kyau dukkan talakawa su yi kyakkyawan amfani da maƙamin na su wajen zabar abun da zai haifa mu su alheri ga rayuwarsu. Kazalika mu na fata na’urar nan ta BVAS da hukuamr zaɓen ta ɓullo da ita don wannan zaɓe za ta taimaka wajen daƙile duk wani yunƙuri na maguɗi ko aringizon ƙuri’a.

Kira ga dukkan jama’a musamman matasa su bi lamura a natsuwa kar su bari a yi amfani da su wajen tada fitina. Tuni har an samu labari a wasu jihohi ’yan sara-suka sun fara bayyana su na shaye-shaye da riƙe makamai don yi wa sauran masu son salama barazana da zummar samun naira. Gaskiya in an duba naira ba ita ce komai ko more rayuwa ba.