Zaɓen 2023: Gwamnati ta tsawaita hutun manyan makarantu

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta tsawaita hutun da ta ba wa manyan makarantu albarkacin zaɓuɓɓukan 2023.

Gwamnati ta tsawai hutun ne sakamakon ɗage zaɓen gwamnoni da na ’yan majalisun jihohi da Hukumar Zaɓe, INEC, ta yi zuwa ranar 18 ga Maris.

Ministan Ilimi, Adamu Adamu ne ya bayyana tsawaita wa’adin hutun, inda ya ce ya zuwa 20 ga Maris, 2023 makarantun da lamarin ya shafa za su koma bakin aiki.

INEC ta ce ta ɗage zaɓen ne domin ba ta damar sake saita na’urorin BVAS da za a yi amfani da su yayin zaɓen na gwamnoni.

Da fari INEC ta shirya gudanar da zaɓen gwamnonin ne a ranar 11 ga Maris, amma yanzu ta ce sai zuwa 18 ga Maris idan Allah Ya kai mu zaɓen zai gudana.