Zaɓen Anambra bai kammalu ba, inji INEC

Daga AISHA ASAS

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa zaɓen gwamna da aka yi shekaranjiya da jiya a Jihar Anambra bai kammalu ba, abin da da Turanci ake kira “inconclusive”.

Hukumar ta ce abin da ya janyo haka shi ne kasa kai ma’aikata da kayan aiki da hukumar ta yi zuwa Ƙaramar Hukumar Ihiala saboda rashin tsaro.

Jami’ar kawo sakamakon zaɓe a zaɓen,
Farfesa Florence Obi, ita ce ta bayyana haka tare da faɗin cewa za a yi zaɓen a ƙaramar hukumar a ranar Talata, 9 ga Nuwamba.

Ya zuwa yanzu dai an bayyana sakamakon zaɓen na ƙananan hukumomi 20 na jihar.

Obi ta ce: “Mun tattara sakamakon zaɓe na ƙananan hukumomi ashirin, amma har yanzu ba a samu na Ihiala ba saboda hukumar ta kasa motsawa a yankin.

“Bisa ga tanadin doka, za a yi zaɓen cikamaki a Ihiala. Saboda haka, za mu gama zaɓen a Ihiala kafin mu kammala komai da komai.

“Ina kira a gare ku da ku mara wa INEC baya don mu samu damar kawo ƙarshen wannan zaɓe, in Allah ya yarda.

“Za a yi zaɓen a Ihiala a ranar 9 ga Nuwamba.”

Ya zuwa daren jiya dai, magoya bayan ɗan takarar zama gwamna na jam’iyyar APGA a zaɓen, Farfesa Chukwuma
Soludo, sun yi tururuwa zuwa ƙauyen Isuofia da ke Ƙaramar Hukumar Aguata, su na rera waƙoƙin taya shi murnar lashe zaɓen jihar tun kafin INEC ta bayyana sakamakon ƙarshe.

Dalili shi ne INEC ta bayyana sakamakon zaɓen a ƙananan hukumomi 20 daga cikin 21 na jihar kuma Soludo, wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya ne, shi ne kan gaban dukkan ‘yan takarar.

A jiya Soludo ya yi kira ga magoya bayan sa da su ci gaba da haƙuri har zuwa lokacin da INEC za ta karanta sakamakon ƙarshe na zaɓen.