Zaɓen fidda gwani: Za mu kwatanta adalci a APC – Adamu

*Shugaban APC ya yi magana kan ɗan takarar masalaha da karɓa-karɓa
*Dokar zaɓe na cigaba da kaɗa hantar gwamnoni
*Yadda ta kaya a zaɓen fidda gwanin PDP a Borno da Yobe
*Kada ku mayar da zaɓen fidda gwani na a-mutu-ko-a-yi-rai, inji Gwamna Masari

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A yayin da jam’iyyun Nijeriya za su ƙarƙare gudanar da zaven fitar da gwani na masu neman kujerar Shugaban Ƙasa a ƙarshen makon nan, Shugaban jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce, jam’iyyar za ta yanke shawara kan batun shiyya-shiyya bayan ta tantance masu neman shugabancin ƙasar a 2023, ya na mai cewa, shugabannin jam’iyyar za su yi ƙoƙarin ganin kowa ya samu adalci a tsakanin masu neman kujerar shugabancin.

Sanata Adamu ya bayyana haka ne a wata hira da wasu kafafen yaɗa labarai na Hausa da suka yi a ranar Laraba, ciki har da Blueprint Manhaja, inda ya ƙara da cewa, za a tantance masu neman shugabancin Nijeriya bisa ƙa’idojin jam’iyyar na zaɓen 2023.

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, ƙa’idojin zaɓe na jam’iyyar sun tanadi hanyoyi guda uku na zaɓen ’yan takararta a zaɓe, waɗanda suka haɗa da; kai tsaye da kuma yarjejeniya.

Da ya ke magana game da shiyya-shiyya na jam’iyyar, Adamu ya ce, ba za a yanke hukunci ba har sai an tantance masu neman ta duka.
“Har yanzu ba mu fitar da ɗan takararmu na shugaban ƙasa ba, dole ne mu tantance masu son mu san hanyar da za mu bi.

Dangane da adadin ‘yan takarar shugaban ƙasa, Adamu ya ce, ba za a iya hana ’ya’yan jam’iyyar damar tsayawa takarar shugaban ƙasa ba.

“Ba za ku iya hana jiga-jigan jam’iyyarmu tsayawa takara ko neman shugabancin ƙasar ba. Haƙƙinsu ne, kuma muna farin ciki a gare su.

Akan yiyuwar jam’iyyar ta amince da irin tsarin da ya samar da shi a matsayin shugabanta, Adamu ya ce, muƙamin shugaban jam’iyyar ba ɗaya ya ke da na shugaban ƙasa ba. Ya jaddada cewa, babu kwatance tsakanin muƙaman biyu.

Ya ƙaryata raɗe-raɗin da ake yi cewa, jiga-jigan masu neman shugabancin jam’iyyar wata dabara ce ta tsawaita wa’adin mulkin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

“Ni dai zan iya cewa Allah zai yi maganin masu irin wannan ɓatanci. Tun a 2019 Shugaba Buhari ya bayyana cewa ba zai nemi a ƙara masa wa’adin mulki ba. Ya gaya wa kowa kuma ya rantse da Alƙur’ani cewa ba zai saɓa wa kundin tsarin mulki ba a wa’adinsa biyu.

Da ya ke magana kan zargin cewa masu neman jam’iyyar na raba kuɗi da wakilai, Adamu ya ce, ba shi da wata hujja a kan hakan. Ya ce, a halin yanzu, duk da haka, babu wata doka da ta hana masu son kai yaƙin neman zaɓen su zuwa wakilai.

Da ya ke da ‘yan takarar gwamna 145 da kuma ’yan takarar shugaban ƙasa 25, Adamu ya bayyana cewa, ’yan siyasa na garzayawa zuwa jam’iyyar APC ne domin ita ce gwamnati mai mulki da kowa da kowa a ƙasar a matsayin mamba.

“Saboda a nan ne abin da ke da muhimmanci a ƙasar. Ba yau aka fara ba; mu ne gwamnati mai mulki. A yau duk da cin mutuncin da ake yi, jam’iyyar APC na da tagomashi a gaban sauran jam’iyyun siyasa.

“A yau jam’iyyar APC ce babbar jam’iyya a Nijeriya. Tana jawo hankalin ‘yan Nijeriya fiye da kowace jam’iyya. A nan ne abin ya ke faruwa. Duk wani ɗan siyasa mai tunani a ɗabi’ance zai koma APC. Tabbas muna da matsalolinmu, amma a yau mu ne silar duk ‘yan Nijeriya, kuma ina fata idan Allah Ya yarda za mu cigaba da riƙe madafun iko a babban zaɓe,” inji shi.