Zaɓen Gwamna: APC tana kan gaba a ƙananan hukumomi 12 cikin 17 a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu

Sakamakon da INEC ta fara tattarawa daga ƙananan hukumomi 12 a cikin 17 dake jihar Yobe, ya nuna jam’iyyar APC da ɗan takararta, Hon. Buni tana kan gaban jam’iyyar PDP da tazara mai yawa.

Da yake bayyana sakamakon zaɓen, Kwamishinan hukumar zaɓe na Jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Abdullahi, ya bayyana cewa ‘yan takara 11 ne suka fafata a zaɓen daga jam’iyyun siyasa daban-daban.

Ya ce a halin yanzu, INEC a Yobe ta karɓi sakamakon zaɓen kananan hukumomi 12 na gwamna a cibiyar tattara sakamakon da ke Damaturu.

Gwamna Buni shi ne ɗan takarar Gwamna a jam’iyyar APC a zaɓen 18 ga watan Maris, 2023.

Bisa ga sakamakon da yake hannu yanzu haka, jam’iyyar APC na kan gaba da ƙuri’u mafi rinjaye fiye da na abokin hamayyarsa, Alhaji Shariff Abdullahi, na PDP.

Ƙananan hukumomin da sakamakonsu ya zo hannun INEC sun haɗa da Tarmuwa, Nangere, Gujba, Gulani, Bursari da Bade.

Sauran su ne Yusufari, Damaturu, Machina, Nguru, Geidam da kuma Yunusari.

Ga yadda sakamakon ya kasance:

Tarmuwa LG
APC – 8,249
PDP -4,145
LP- 06
NNPP- 85

Nangere LG
APC – 18,346
PDP – 6,958
LP -17
NNPP -450

Gujba LG
APC – 20,258
PDP – 2,428
LP -08
NNPP -46

Gulani- LG
APC – 16,244
PDP – 5,537
LP -05
NNPP-115

Bursari LG
APC 13,825
PDP 4,879
LP -11
NNPP -97

Bade LG
APC – 21,370
PDP- 10,766
LP -18
NNPP -1254

Yusufari LG
APC- 16,216
PDP- 3,837
LP -19
NNPP -222

Damaturu LG
APC -20877
PDP- 7,655
LP -22
NNPP -217

Machina LG
APC-11,039
PDP- 4,288
LP- 18
NNPP- 262

Nguru LG
APC- 22,459
PDP- 9,332
LP- 18
PDP -9332

Geidam LG
APC – 14495
PDP- 1777
LP- 10
NNPP -355

Yunusari LG
APC-16,042
PDP- 2,102
LP-27
NNPP-1,657