Zaɓen gwamnoni: A ina za a iya yin ‘inconclusive’ bana?

*Ba a san maci tuwa ba..!

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Gobe ake gudanar da zaɓen gwamnoni da na majalisar dokoki na jihohi a Tarayyar Nijeriya, waɗanda ake sa ran rantsarwa a ranar 29 ga Mayu, 2023, bayan kammala wa’adin zangon gwamnoni da ’yan majalisar dokoki na jihohi.

Zaɓen da ya gabata na 2019 ya zo da wani sabon salon ƙa’idar da ba a saba gani ba a zaɓukan baya, inda ba a sanar da sakamakon zaɓe bisa dalilin wata kalma ta ‘inconclusive’, wacce ta ke nufin ‘rashin kammaluwa’ ko kuma ‘zaɓen da bai kammalu ba’.

Shin mene ne ‘Inconclusive’?

Kalmar ‘inconclusive’ ta shahara ne a zaɓukan 2019, inda Hukumar Zave Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ke ƙin bayyana sakamakon ƙarshe na zaɓe, idan yawan ƙuru’un da aka soke ko suka lalace sun fi yawan ƙuri’un da ɗan takarar da ke kan gaba ya bai wa mai biye da shi. A cewar Hukumar INEC, ba ta da hurumi ko ikon ayyana wanda ya lashe zaɓen har sai an sake gudanar da zaɓe a akwatunan da aka soke waɗancan lalatattu ko sokakkun ƙuri’u.

Shin me ya faru a zaɓen 2019?

A zaven jihohi na 2019, an samu jihohi guda shida, waɗanda sakamakon zaɓukansu suka kasa kammaluwa, inda har sai da aka tafi zaɓukan ‘inconclusive’. Jihohin kuwa sun haɗa da Adamawa, Bauchi, Benuwe, Filato, Kano da Sokoto, waɗanda dukkanninsu a Yankin Arewa suke.

A Jihar Adamawa, Jam’iyyar PDP da ɗan takararta Umaru Fintiri sun samu ƙuri’a 367,471 a zagayen farko, inda Jibrila Bindow na APC ya samu 334,995, wanda hakan ke nuni da bambancin ƙuri’a 32,476. To, amma an soke ƙuri’a guda 40,988, waɗanda sun fi ratar da ke tsakanin na ɗaya da na biyu kenan.
Bayan zuwa zaɓen ‘inconclusive’, a ƙarshe dai PDP ta lashe zaɓen, inda ta kayar da gwamna mai ci na wancan lokaci, wato Bindow.

A Jihar Bauchi ma Jam’iyyar adawa ta PDP a lokacin, wacce Bala Mohammed ke yi wa takara, ce ke kan gaba, inda ta ke da ƙuri’a 469,512, ita kuma APC ke da 465,453 a ƙarƙashin takarar Gwamna Mohammed Abubakar. Hakan ya nuna an samu ratar ƙuri’a 4,059 kenan, amma ƙuri’un da aka soke sun kai guda 45,312.

Bayan gudanar da ‘inconclusive’, nan ma PDP ta samu nasara.

A Jihar Benuwe, PDP, wacce Gwamna Samuel Ortom ke yi wa takara, na da ƙuri’a 410,576 a zagayen farko, yayin da Emmanuel Jime na APC ke da 329,022, wanda ke nuna cewa, akwai ratar ƙuri’a 81,554 kenan, amma an soke guda 121,019.

Bayan kammala ‘inconclusive’, a nan ma ɗin dai PDP ce ta samu nasarar lashe zaɓen.

Ita kuwa Jihar Kano yadda abin ya wakana shine, Abba Yusuf na PDP ne akan gaba da ƙuri’u 1,014,474, yayin da gwamna mai ci, Abdullahi Umar Ganduje, ke biye masa da ƙuri’a 987,819, wanda hakan ke nuni da ratar ƙuri’a 26,655. Amma an soke ƙuri’u guda 128,572.

Sai dai kuma saɓanin a jihohin da muka ambata, a Kano APC ce ta lashe zaɓen bayan da aka gudanar da zaɓen ‘inconclusive’.

A Jihar Filato, APC ce akan gaba, wacce Gwamna Simon Lalong ke yi wa takara da ƙuri’a 583,255, inda Jerry Useni na PDP ke biye masa da quri’a 538,326, wanda hakan ke nuni da ratar ƙuri’a 44,929. To, amma ba a nan gizon ke saƙa ba, domin an soke ƙuri’a 49,377.

Bayan kammala zaɓen ‘inconclusive’, APC ta lashe zaɓen ne a nan ma ɗin.

A Jihar Sokoto kuwa, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na PDP ne akan gaba da ƙuri’a 489,558, yayin da Aliyu Ahmed na APC ke biye masa da ƙuri’u 486,145, wanda hakan ke nuni da ratar ƙuri’a 3,413 kacal. Amma an soke ƙuri’u har guda 75,403.

Bayan gudanar da zaɓen ‘inconclusive’, PDP ta ƙarasa samun nasara.

Shin a ina za a sake yin ‘inconclusive’?

Kamar yadda muka ambata a baya, a Arewa ne kaɗai aka samu zavukan gwamnonin da ba su kammala ba har sai da aka tafi zagaye na biyu sakamakon lalacewar ƙuri’u, to amma yanayin yadda aka gudanar da zaɓen Shugaban Ƙasa a Jihar Legas na nuni da cewa, za a iya samun ‘inconclusive’ a karo na farko a Yankin Kudu.

Haka nan sakamakon yadda zaɓen ’yan Majalisar Dokoki Ta Tarayya ya kasance a Jihar Sokoto lokacin da aka gudanar da shi tare da na Shugaban Ƙasa mako uku baya, inda dukkanninsu suka zama ‘inconclusive’, hakan na nuni da cewa, ba abin mamaki ba ne, idan a zaɓen gwamna ma aka samu rashin kammaluwar zaɓen.

A Jihar Kano ne aka fi samun cece-kuce a zaɓen ‘inconclusive’ da aka gudanar a 2019. Don haka daga dukkan alamu shi aka zuba wa idanu a ga yadda za ta kaya.

Ba a san maci tuwo ba, sai miya ta ƙare!