Zaɓen Gwamnoni: A jihohi 28 kaɗai za a fafata

Daga BASHIR ISAH

Jihohi 28 daga cikin 36 da Nijeriya ke da su ne za a gudanar da zaɓen gwamnoni ran Asabar, 18 ga Maris, 2023.

Yayin da zaɓen gwamnonin ba zai gudana ba a wasu jihohi guda takwas da suka haɗa da Anambra, Bayelsa, Edo, Ekiti, Imo, Kogi, Osun da kuma Ondo, waɗanda sukan gudanar da nasu a lokuta na daban saboda hukuncin kotu da ya gitta.

Jihohin da za su shaida zaɓen gwamnonin a wannan Asabar, sun haɗa da:

Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Bauchi, Binueai, Borno, Kuros Riba, Delta, Ebonyi, Enugu, Gombe, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kwara, Lagos, Nassarawa, Neja, Ogun, Oyo, Filato, Ribas, Sakkwato, Taraba, Yobe da kuma Zamfara.

Sai dai, zaɓen majalisun jihohi zai gudana a duka jihohi 36 a faɗin ƙasar.