Zaɓen sabbin shugabannin ƙungiyar MOPPAN ya zo da sabon salo

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano 

Haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwararru ta masu shirya fim ta ƙasa, wato ‘Motion Picture Practitioners Associations of Nigeria’ (MOPPAN), ta gudanar da zaɓen sabbin shugabanninta bayan kammala wa’adin shugabancin shugabannin na tsawon shekaru biyu, kamar yadda tsarin mulkin ƙungiyar ya tanada.

Zaɓen dai an gudanar da shi ne a ranar Juma’ar da ta gabata a babban ɗakin taro na otel ɗin Ni’ima da ke cikin garin Kano.

Taron, wanda kafin gudanar da shi aka fara da Babban Taron Ƙungiyar na Ƙasa, wato ‘Congress’, wanda a lokacin aka yi zaman Gyaran Kundin Tsarin Mulkin Ƙungiyar, inda aka shafe tsawon dare tare da muhawara mai zafi. 

Wani sabon salo da zaɓen da ƙungiyar MOPPAN ɗin ya zo da shi kuwa, shi ne, a na shirin kaɗa ƙuri`a, sai ga saƙon takarda daga ’yan takarar, wacce ta ke ɗauke da sanyya hannunsu cewar, duk wani matsayin da suke nema a kujerar shugabancin, to masu takarar ba su da abokan karawa. Saboda haka sun yi masalaha a tsakaninsu, wato ba sai an shiga zaɓe ta hanyar kaɗa ƙuri’a ba.

Don haka kowa ya ci zaɓen kujerar da ya ke takara, illa kawai su na neman sahalewar kwamitin zaɓen, idan har ya amince da hakan, ba sai an je ga kaɗa ƙuri’a ba. Su kuma ‘yan kwamitin zaɓe suka amince da hakan. Don haka kowa ya ce babu hamayya, illa kawai ’yan kwangures su amince, wanda shi ma nan take, su ka amince musu.

Haka nan kuma Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ne da kansa ya jaoranci rantsar da sababbin shugabannin na MOPPAN, domin bayan kammala zaɓen ne a ranar Asabar, sai kuma aka yi bikin rantsar da su a ranar Lahadi a babban ɗakin taro na ‘Coronation Hall’ da ke Gidan Gwamnatin Jihar Kano.

A lokacin da zaɓaɓɓun shugabannin MOPPAN na ƙasake shan rantsuwa a ‘Coronation Hall’ da ke Gidan Gwamnatin Kano

Shugabannin da aka zaɓa dai su ne:
Dakta Ahmad Sarari a matsayin Shugaba, sai Malam Habibu Barde a matsayin Mataimakin Shugaba na Arewa ta Tsakiya da Ibrahim Amarawa a Mataimakin Shugaba na Arewa maso Gabas, sai kuma Umar Maikuɗi Cashman a matsayin Mataimakin Shugaba a Arewa maso Yamma. Salisu Mu’azu a matsayin babban sakataren ƙungiyar. Umar Gombe a Mataimakin Sakatare, sai Fatima Lamaj a matsayin Sakatariyar Kuɗi, Al’amin Ciroma shine ya sake zama Jami’in Yaɗa Labarai na I, inda Mustapha Badamasi Naburaska ya zama Jami’in Yaɗa Labarai II. Maijidda Abbas kuma Jami’ar Walwala, sai Ibrahim I. Ibrahim a Mai Binciken Kuɗi na I (Auditor I), sai kuma Bello Achida a Mai Binciken Kuɗi na II.

Da ya ke jawabi bayan rantsar da su da aka yi, sabon shugaban ƙungiyar kuma shugabanta a karo na biyu, Dakta Ahmad Sarari, ya yi alƙawarin sauke nauyin da aka ɗora masa tare da yin kira ga ‘yan ƙungiyar da su ba shi goyon baya, domin ya cimma nasara a kan alƙawarin da ya ɗauka.

Daga nan ne Gwamnan Jihar Kano ya jagoranci ’yan ƙungiyar, inda aka ɗunguma zuwa cikin Fadar Gwamnatin Jihar, wato Africa House, wajen da gwamnan ya shirya musu ƙayatacciyar liyafar cin abincin dare.