Za a ƙaddamar da cibiyar watsa labaru ta taron wakilan JKS karo na 20 a ranar 12 ga watan Oktoba

Daga CMG HAUSA

Za a ƙaddamar da cibiyar watsa labaru ta babban taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta Sin wato JKS karo na 20, a ranar Larabar makon gobe wato 12 ga watan Oktoban nan, tare da karɓar ‘yan jarida a hukumance.

An kafa sashen karɓar ‘yan jarida, ta cibiyar, a otel din Nikko New Century dake nan birnin Beijing.

Cibiyar watsa labaru ta taron, za ta samar da hidima ga ‘yan jarida daga yankin Hong Kong, da na Macau, da na Taiwan, da kuma na ƙasashen waje, da za su watsa labaru game da taron, a fannonin samar musu takardun iznin watsa labaru, da karbar rokon watsa labarun, kana cibiyar za ta gudanar da taron manema labaru, da kuma shiryawa ‘yan jaridar da su shiga taron damar watsa labaru.

Za a ƙaddamar da shafin internet na cibiyar, wato http://20th.cpcnews.cn, da kuma sauran shafunan dandalin internet, a ranar 10 ga wannan wata a hukunce, a lokacin za a ba da labarai, da sanarwa game da taron, da kuma taron manema labaru kai tsaye.

Kana an tanadi reshen musamman na shafin cibiyar, don samar da hidima ga ‘yan jarida a ciki da wajen ƙasar Sin, da suka yi rajistar watsa labaru game da taron.

Fassarawar Zainab

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *