Za a ƙaddamar da littafin salatin Annabi a ranar Asabar a Kano

Daga FATUHU MUSTAPHA

A ranar Asabar mai zuwa, 20 ga Fabrairu, 2021, za a ƙaddamar da wani littafi da aka wallafa a kan salatin Annabi Muhammadu (SAW) a Kano.

Littafin, mai taken ‘Salatin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Sallam: Matsayinsa Da Fa’idojinsa Da Sigoginsa’, wata marubuciya mai suna Hajiya Hajara Muhammad Kabir ce ta wallafa shi.

Ɗan kwamitin yaɗa labarai na shirya taron, Malam Ibrahim Sheme, ya bayyana cewa za a ƙaddamar da shi ne a fadar Mai Martaba Sarkin Kano da ƙarfe 10 na safe.

A cikin takardar sanarwa ga manema labarai, Sheme ya ce manyan baƙi daga sassa daban-daban na ƙasar nan ne za su halarta a ƙarƙashin jagorancin uban taron, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, yayin da Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, shi ne mai gayyata.

Ya ƙara da cewa Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje (Khadimul Islam), zai kasance babban baƙo na musamman.

Shugaban taron shi ne tsohon gwamnan Kano kuma Sardaunan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau.

Sheme ya ce masu ƙaddamarwa su ne shahararrun ‘yan kasuwar nan, Alhaji Aminu Ɗantata, Alhaji Aliko Ɗangote, Alhaji Abdulsamad Isyaka Rabi’u da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar.

Sanarwar ta ƙara da cewa Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau na Jami’ar Bayero, Kano, shi ne zai yi bitar littafin a wajen taron.

Bugu da ƙari, ya ce da yake ana yaƙi da annobar korona ne yanzu, masu shirya taron sun tsara wajen taron yadda za a kiyaye dukkan ƙa’idojin da hukuma ta gindaya na hana kamuwa da cutar.

Marubuciyar littafin, Hajiya Hajara Muhammad Kabir, ‘yar asalin Kano ce wadda ta samu digirin farko a fannin nazarin Hausa daga Jami’ar Bayero, Kano.

Haka kuma ita ce mawallafiyar mujallar nan mai suna ‘Goshi: The Fortuna Magazine’.

Littattafan da ta wallafa sun haɗa da ‘Northern Women Development: A Focus on Women in Northern Nigeria’, wanda aka buga a cikin 2010.

A kan manufar wannan sabon littafin nata mai shafi sama da 175 da za a ƙaddamar, Hajiya Hajara ta bayyana cewa ta rubuta shi ne domin ta zaburar da al’ummar Musulmi baki ɗaya su san fa’idoji da sigogin salatin Annabi kuma su yi riƙo da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *