Za a ƙara samar da motocin dake amfani da sabbin makamashi a Sin

Daga CMG HAUSA

Jami’in ma’aikatar sufuri ta ƙasar Sin Li Guoping ya bayyana cewa, gwamnatin ƙasar za ta ƙara samar da goyon baya ga sana’ar ƙera motoci da fasahohin zamani dake amfani da sabbin makamashi.

Jami’in ya bayyana haka ne bayan rufe babban taron motoci masu amfani da sabbin makamashi na duniya a jiya Lahadi.

Li Guoping yana mai cewa, mataki na gaba shi ne nazari da tsara tsarin rage fitar da sinadarin carbon, kuma za aiwatar da manufar bayar da tallafi don yayata amfani da motoci masu amfani da sabbin makamashi.

Li Guoping ya nuna cewa, ma’aikatar sufuri za ta gudanar da ayyukan da suka shafi motoci masu amfani da sabbin makamashi da fasahohin kwaikwayon tunanin bil Adam, da ƙarfafa nazarin muhimmiyar fasahar sufuri mai basira da sufuri mai kiyaye muhalli, don samar da tallafin kimiyya da fasaha.

Mai fassarawa: Safiyah Ma daga CMG Hausa