Za a ɗage dakatarwar da aka yi wa Ningi ba da daɗewa ba – Akpabio

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa, nan ba da daɗewa ba za a ɗage dakatarwar da aka yi wa Sanata Abdul Ningi (PDP, Bauchi ta Tsakiya) a Majalisar Dattawa.

Ya bayyana hakan sa’ilin da yake amsa wa manema labarai tambayoyi a wajen wani taro da aka shirya ranar Juma’a a Geneva, Switzerland.

Wannan na zuwa ne sa’o’i 24 bayan da Ningi ya yi wa Akpabio kan cewa zai ƙalubalanci dakatar da shi da aka yi a kotu muddin ba a janye dakatarwar ba a cikin kwana 7.

An dakatar da Ningi daga majalisar ne biyo bayan hirar da BBC Hausa ta yi shi inda ya bayyana cewa an yi cushen Naira tiriliyan 3.7 a kasafin 2024.

Lamarin da ya haifar da zazzafar muhawara a sassan ƙasa, musamman a Majalisar Dattawa wanda a ƙarshe ya kai ga majalisar ta ɗauki matakin dakatar da Ningi daga shiga majalisar na tsawon wata uku.

Sai dai kuma, a cikin wasiƙar da Ningi ya aike wa Akoabio ta hannun lauyansa, Femi Falana (SAN), Sanatan ya zargi Akpabio kan cewa shi ɗin ne abin zargi.

Ningi ya zargi Akpabio kan haddasa ya zama abin zargi a gaban majalisar a ranar 14 ga Maris, 2024, wanda a cewarsa hakan ya saɓa wa Dokar Majalisar Dokoki ta 2018.