Za a buɗe hanyar saida sabbin layukan sadarwa 19 ga Afrilu, cewar Gwamnati

Daga AISHA ASAS

Gwamnatin Tarayya ta bada sanarwar cewa ya zuwa ranar 19 ga Afrilun da muke ciki za a buɗe hanya don bada famar mallakar sabon layin sadarwa (SIM CADR) ga masu buƙata.

Gwamnatin ta ce hakan zai tabbata ne bayan kammala tantancewa da kuma tabbatar da kiyaye dokoki yadda ya kamata.

Ma’aikatar Sadarwa da Tattalin Arzikin Intanet ita ce ta yi wannan bayani a wata sanarwar manema labarai da ta sami sa hannun hadimini ministan sadarwa, Femi Ademiluyi.

Idan dai za a iya tunawa a Disamban 2020 ne gwamnati ta dakatar da saida layukan sadarwa da nufin tantance bayanan jama’a da ke maƙale da layukan na sadarwar da ake amfani da su a faɗin ƙasa.

Ma’aikatar Sadarwa ta ce shirin binciken da tantancewar na da muhimmaci saboda zai taimaka wajen tabbatar da cewa kamfanonin sadarwa na bai wa jama’a haƙƙinsu yadda ya kamata, sai kuma ingantawa tare da tsaftace hanyar da ake bi wajen yi wa layi rajista.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*