Za a fara allurar rigakafin korona a Nijeriya cikin Maris

Daga AISHA ASAS, Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ce, ana sa ran a soma allurar rigakafin cutar korona ya zuwa karshen Maris ko Afrilun 2021.Ministan Lafiya, Osagie Ehanire ne ya bayyana haka sa’ilin da Kwamitin Shugaban Kasa Kan Yaki da COVID-19 (PTF) ke gabatar da bayanin ayyukankasa, Litinin da ta gabata a Abuja.

Ehanire ya ce, “Adadin maganin da Nijeriya ta yi odar sa ta AVATT na Hukumar Hada Kan Afirka, ya danganci daidai adadin da ake bukata ne don gundun barna.”

Ya ci gaba da cewa, Nijeriya na yin dukkan maiyiwuwa don tabbatar da an yi wa akalla kashi 70 cikin 100 na ‘yan Nijeriya allurar rigakafin ya zuwa 2023.

Jaridar Manhaja ta nakalto Ministan na cewa, “Muna tattaunawa da bangarori daban-daban domin samar da tsare-tsaren da za su taimaka wajen aiwatar da rigakafin ta hanyar lura da matakan baya-bayan da aka yi amfani da su wajen kawar da cutar Polio.

“Baya ga magani guda 100,000 da kamfanin COVAX ya bai wa Nijeriya, gwamnati ta sake neman wasu guda milyan 10 daga AVATT.”

Ehanire ya karasa da cewa, “Nijeriya na da allurar rigakafin da ta samar wadda ke bukatar a zuba jari mai ma’ana don iya kaiwa ga matakin gwaje-gwaje. Za mu yi kokarin neman wadanda za su dauki nauyin aikin domin a samu a kai ga gaci.”