Daga MAHDI M. MUHAMMAD
A ƙarshen watan Oktoba ne Gwamnatin Tarayya za ta fara biyan kuɗaɗen kason ƙananan hukumomi kai tsaye, a cewar Ambali Olatunji, Shugaban ƙungiyar Ma’aikatan ƙananan Hukumomi ta ƙasa (NULGE).
A wata hira da manema labarai, Olatunji ya tabbatar da cewa, a wannan watan ne za a fara aiwatar da shirin samar da ’yancin cin gashin kan harkokin kuɗi na ƙananan hukumomi, wanda ke nuna gagarumin sauyi kan yadda ƙananan hukumomi za su samu kuɗaɗen su kai tsaye.
Wannan matakin dai ya biyo bayan wani gagarumin hukunci da Kotun ƙoli ta yanke a watan Yuli, inda mai shari’a Emmanuel Agim ya bayyana cewa bai dace ba gwamnonin jihohi su riƙe kuɗaɗen da ake ware wa aananan hukumomi.
Kotun ta jaddada cewa ƙananan hukumomi da aka zaɓa ta hanyar dimokuraɗiyya ne kaɗai aka amince da tsarin mulkin ƙasar, wanda hakan ya sa ya hana gwamnatocin jihohi naɗa kwamitocin riƙo.
Gwamnonin jihohin da tun farko suka bijirewa hukuncin, sun buƙaci a ba su wa’adin watanni uku domin shirya zaɓen ƙananan hukumomi. Tare da tsawaita wa’adin ya ƙare a watan Satumba, tsarin rarraba kuɗaɗe kai tsaye ya shirya don fara aiki.
Olatunji ya bayyana fatansa cewa wannan cin gashin kansa na harkokin kuɗi zai inganta ƙarfin ƙananan hukumomi wajen isar da muhimman ayyuka da kuma magance ƙalubalen ci gaban da al’ummarsu ke fuskanta.
Ya ƙara da cewa, “A ranar 11 ga watan Oktoba, za a fara aiwatar da ’yancin cin gashin kan harkokin kuɗi ga ƙananan hukumomi. Muna sa ran nan da ƙarshen watan Oktoba, asusun kansiloli a faɗin ƙasar nan za su karɓi kason su kai tsaye.”
NULGE ta kuma miƙa shawarwari kan yadda ake tafiyar da ƙananan hukumomi ga kwamitin ƙwararru na Gwamnatin Tarayya da ke da alhakin kula da harkokin cin gashin kai.
Olatunji ya kuma buƙaci gwamnatocin tarayya da na Jihohi da su aiwatar da matakan kariya don hana karkatar da waɗannan kuɗaɗe daga mahukuntan kansilolin.
Ana sa ran wannan ci gaban zai samar da ingantaccen aiki da gaskiya a harkokin gudanar da mulki a faɗin Nijeriya, wanda zai iya haifar da wani sabon zamani na ingantacciyar ci gaban ƙasa.