Za a fara rajistar masu zaɓe a ranar 28 ga Yuni

Daga WAKILINMU

Hukumar Zaɓe mai Zaman Kan ta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa za a ci gaba da aikin rajistar katin masu zaɓe a ranar 28 ga Yuni, 2021.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a taron da ya yi da su a hedikwatar hukumar a Abuja a ranar Alhamis.

Mahmood ya ce, “Bayan mun duba waɗannan matsaloli da matakan da mu ka ɗauka don magance su, yanzu hukumar ta kai matsayin da za ta iya bayyana Litinin, 28 ga Yuni, 2021 a matsayin ranar da za mu koma mu ci gaba da rajistar katin zaɓe (CVR) a duk faɗin ƙasar nan.”

Ya ce za a ci gaba da gudanar da aikin har zuwa kashi na uku na shekarar 2022.

Wannan aiki, kamar yadda aka tsara a Sashe na 10 na kundin Tsarin Mulkin Nijeriya, za a ci gaba da yin sa babu yankewa to amma hakan ba ta yiwu ba saboda “matsalolin rashin abin hannu.”

Yakubu ya ce ba a iya ci gaba da aikin ba ne yawanci saboda matsalar nan ta cutar korona (COVID-19).

A yayin da ya ke tunowa da yunƙurin da hukumar ta sha yi don tabbatar da ci gaba da rajistar masu zaɓe, shugaban ya ce an yi aikin CVR ɗin babu yankewa daga Afrilu 2017 har zuwa ƙarshen Agusta 2018 lokacin da aka ɗan ɗage shi a lokacin da ake shirye-shiryen Babban Zaɓen shekarar 2019.

Ya ce: “Abin da ya biyo bayan Babban Zaɓen kuma kamar yadda aka saba yi shi ne al’amura daban-daban na hukumar, kamar su shari’un bayan zaɓe, nazarin bayan zaɓe, da kuma zaɓuɓɓukan da ba su cikin tsari daban-daban, musamman zaɓuɓɓukan gwamna a jihohin Kogi da Bayelsa, waɗanda aka yi a ƙarshen 2019.

“Irin waɗannan zaɓuɓɓukan tilas ne a gudanar da su tare da yin amfani da Rajistar Masu Zaɓe da aka yi amfani da ita a Babban Zaɓen 2019.

“An kasa ci gaba da aikin CVR a cikin 2020 yawanci saboda annobar korona. Don bin shawarar da jami’an kiwon lafiya su ka ba kowa a kan tarurrukan da ake haɗa gungun mutane masu yawa, mun yanke shawarar cewa bai dace a ci gaba da aikin CVR ba a daidai lokacin da ake kan ƙololuwar annobar.

“Hukumar ta fitar da cikakken tsari kan yadda za a gudanar da zaɓuɓɓukan a lokacin annobar korona, wanda ya maida hankali ga yin zaɓe da ya dace, tunda dai tilas ne a yi zaɓuɓɓukan don kauce wa duk wani rikicin saɓa wa kundin tsarin mulki da za a danganta shi da ƙarewar wa’adin mulki. An yi irin waɗannan zaɓuɓɓukan a jihohin Edo da Ondo a ƙarshen shekarar da ta gabata.

“Tunanin mu a lokacin shi ne a farkon shigowar wannan shekara za mu samu damar kammala dukkan zaɓuɓɓukan da su ka rage, waɗanda ba su cikin kakar zaɓe kuma annobar korona za ta ragu.

“Kuma a lokacin mu na buƙatar lokacin da za mu sanya sababbin tsare-tsare da za su taimaka a yi aikin rajistar masu zaɓe cikin kare lafiya idan annobar ta ci gaba da wanzuwa.”

Shugaban na INEC ya ce da farko an tsara cewa za a fara ci gaba da aikin ne a cikin wata uku na farkon shekarar 2021.

Yakubu ya ce yanzu dai hukumar ta gama shirin soma aikin a ranar 28 ga Yuni kafin a yi zaɓen gwamnan Anambra na shekarar 2012.

Ya ce za a yi shekara ɗaya ana aikin har zuwa cikin kashi na uku na 2022 tare da maida hankali kan Jihar Anambra saboda zaɓen gwamnan jihar wanda za a yi a ranar 6 ga Nuwamba.

Ya ce, “Daga ranar Litinin, 28 ga Yuni, 2021, za a fara aikin CVR a duk faɗin ƙasar nan kuma za a dinga yin sa ba tsayawa har sama da shekara ɗaya, har zuwa cikin kashi na uku na 2022.

“Amma da farko za a maida jankali kan Jihar Anambra inda za a buɗe ƙarin cibiyoyi saboda zaɓen gwamna da aka riga aka tsara yi a ranar Asabar, 6 ga Nuwamba, 2021.

“Domin a kammala shirye-shiryen zaɓen gwamnan, za a ɗan ɗage aikin CVR a jihar a cikin Agusta 2021. Hakan zai ba hukumar damar ta share bayanan jihar sannan ta buga katittikan zaɓe saboda masu yin rajista.

“Bayan wani lokaci, hukumar za ta samar da ƙarin bayani kan aikin CVR ɗin, musamnan sababbin dabarun da aka zo da su domin masu zuwa yin rajista su yi komai cikin kare lafiya kuma cikin sauƙi. Don yin hakan, za mu yi tuntuɓa sosai da dukkan masu ruwa da tsaki. Hasali ma dai, tuntuɓar farko da za mu yi za mu fara ta ne bayan hutun Ista.”

Yakubu ya kuma bayyana cewa injin da ake amfani da shi a da ana tantance mai zaɓe wanda ake kira ‘Direct Data Capturing Machine’ (DDC), yanzu za a maye gurbin sa ne da wasu ƙananan na’urorin komfuta don samun ƙarin sauƙi a lokacin zaɓe.

Sabuwar na’urar ana kiran ta ‘INEC Voter Enrolment Device’ (IVED) kuma an yi ta ne bisa tsarin ƙaramar komfutar ‘tablet’ mai aiki da tsarin Android.