Za a fara sanya jaruma Sola Sobowale a fim ɗin Indiya

Daga AISHA ASAS

Fitacciyar jaruma a masana’antar fim ta Kudu wato Nollywood, Sola Sobowale ta yi tsalle mai tsayi, inda ta samu nasarar samun aikin fim daga Ƙasar Indiya.

Jarumar wadda aka fi sani daToyin Tomato ce ta bayyana hakan a shafinta na Instagram. Inda ta bayyana tafiyar da zata yi Ƙasar Indiya domin aiki da sananniyar mai shirya fim Hamisha Daryani Ahuja, a wani fim da za a fara aikinsa.

“Ina farin cikin sanar da ku cewa, zan yi tafiya zuwa Ƙasar Indiya don aiki tare da shaharariyyar darakta kuma furodusa Hamisha Daryani Ahuja, a aikin fim ɗin da zata gudanar. Zan taka rawa ta musanmman a fim ɗin, wanda na ke da tabbacin zai ƙayatar da ku. Ko kun yi murna kamar yadda na ke yi?”

Jaruma Sola Sobowale ta jima tana bada gudunmawa a cigaban masana’antar Nollywood, kuma ta kasance ɗaya daga cikin dattijai a masana’antar da har yau zarensu bai tsinke ba.

Ƙwarewar Sole ya sanya ake haska ta a manyan finafinai da suka yi fice, inda ta kasance ɗaya daga cikin jaruman da ke ƙayata shararren shirin nan mai dogon zango da ya samu masoya a ciki da wajen Nijeriya wato ‘King of boys’. Shirin da ya yake bayyana irin dambawar da ke cikin siyasar Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *