Daga BASHIR ISAH
Hukumomin Saudiyya sun bayyanar da harsunan da za a fassara Huɗubar Arfa yayin aikin Hajjin 2023.
Sanarwar hukumomin ta nuna manyan harsunan duniya guda 20 ne za a fassara huɗubar a cikinsu, ciki har da harshen Hausa.
Shugaban kula da masallacin Ka’aba da na Annabi da ke Madina, Sheikh Dr. Abdulrahman Al-Sudais ne ya bayyana haka, yana mai cewa an kammala dukkan shirye-shirye domin yaɗa huɗubar kai tsaye daga Masallacin Namirah.
A cewarsa, harsunan da lamarin ya shafa sun haɗa da: Hausa, Faransanci, Ingilishi Persian, Urdu, Russian, Turkish, Punjabi, Sinan i, Malayo, Swahili, Spanish, Portuguese, Amharic, Jamussanci, Swedish, Italian, Malayalam, Bosnian da kuma Filipino.
Ya ce za kuma a iya samun Huɗubar a manhajar ‘Arafat Sermon’ da ma dandalin Manarat Al-Haramain.
Sheikh Al-Sudais ya ce wannan aikin shi ne irinsa mafi girma a duniya wanda bana shi ne karo na uku da fara aiwatar da shi.