Za a ga bambanci a zaɓen 2023

Ko shakka babu a zaɓe mai zuwa na 2023 dole ne a ga zahirin bambanci na zaɓen 2015 da 2019 a yadda wannan zaɓe zai wakana a nau don nazarin ƙuri’un Kudu za su ninka na baya domin a wajensu dama ce ta zo.

Kar mu manta da cewa a Arewa ce kaɗai za a samu ga mutane rututu duk sun wuce shekaru 18 amma da dama sun ƙi mallakar katin zaɓe PVT wasu kuma sun mallaka amma sai su ƙi zuwa yin zaɓen inda wasu kuma a ranar zaɓen ƙuri’arsu ta sayarwa ce duk wanda ya miƙo kuɗi sun sallama.

A kudanci irin waccen ɗabi’a ba ta da yawa a cikin su. Ɗan siyasar Arewa ya fi son ya tara kuɗi idan kun je maula ya ɗan tsakuro kaɗan ya ba da.

Ɗan siyasar Kudu ya fi siyasa ta kishi da manufa kuma ta gina al’umma.

Duka waɗannan ababen lura ne amma idan an nutsu. Zaɓe zai zo da sabon salo na kishi da manufa a kudanci inda mu kuma da dama siyasar mi zan samu ita a ke yawan yi tun daga ’yan takarar har zuwa talakawan. Allah kaimu mu zaɓi na kwarai.

Daga Mukhtar Ibrahim saulawa. 07066434519 – 08080140820.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *