Za a garƙame ku idan ku ka saci kuɗin ƙananan hukumomi – Antoni Janar ga ciyamomi

Daga BELLO A. BABAJI

Antoni-Janar na Ƙasa (AGF) kuma Ministan Shari’a, Frins Lateef Fagbemi (SAN) ya jaddada gargaɗi ga ciyamomi game da sata ko sauya aƙalar kuɗaɗen asusun ƙananan hukumominsu.

Fagbemi ya bayyana hakan ne a Abuja, a ranar Alhamis, yayin taron Ƙungiyar Manema labarai na Ɓangaren Shari’a (NAJUC) da aka saba yi a duk shekara, inda ya yi nuni da muhimmancin tabbatar da gaskiya da adalci a yayin ayyukansu tare da tsoratar da su game da haɗarin dake cikin sace dukiyar ƙaramar hukuma wanda ya ce hakan ka iya sanya doka ta yi aiki akan duk wanda aka kama tare da tasa ƙeyarsa zuwa gidan yari.

Ministan ya ce damar cin gashin kai da Kotun Ƙoli ta bai wa ƙananan hukumomin ya samu ne don inganta harkokin gudanar da shugabancinsu.

Ya nuna damuwa kan yadda wasu ka iya amfani da damar cin gashin kan wajen azurta kawunansu, ya na mai alƙawarin ɗaukar mataki akan duk wanda aka kama da cin amanar ƙaramar hukumarsa.

Ya kuma yi kira ga ciyamomin da su mayar da ayyukan ci-gaba a yankunansu su zamo su ne abubuwan da suka saka a gaba don amfanar da al’ummominsu.

Haka nan Antoni-Janar Fagbemi ya koka kan yadda gwamnonin wasu jihohi ke ƙoƙarin daƙile ƴancin cin gashin kan da aka bai wa ƙananan hukumomin inda ya tunatar da su hukuncin Kotun Ƙoli game da hakan.

Har’ilayau, Fagbemi ya yaba wa Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ƙoƙarin samar da ingantaccen tsarin shugabanci a kowane mataki, ya na mai kira ga jami’an ƙananan hukumomi da su kasance masu adalci yayin gudanar da ayyukasu.