Daga BELLO A. BABAJI
Rundunar ƴan sanda ta ce duk wanda ya haura shekara 7 ya cancanci a maka shi kotu.
Kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi ya faɗi hakan a ranar Juma’a yayin wata hira da gidan talabijin na ‘channels’ inda ya bayyana hukuncin doka da ya bada damar kai wanda ya haura shekara bakwai kotu tare da bin hanyoyin da dokar ta tsara.
Kakakin ya bayyana hakan ne yayin da ake tsaka da cecekuce game da batun kama wasu yara da ake zargin su da hannu a laifukan haddasa tashin-tashina a lokacin da aka gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a watan Agusta.
Ya ce, ƙarami daga cikin waɗanda aka kama shi ne ɗan shekara 13, sannan ko a dokar yara da ƙananan yara, akwai jawabin da ya bada damar maka su a kotu.
Ya ƙara da cewa, waɗanda aka kama, matasa ne da suka sauya zanga-zangar tsadar rayuwa zuwa tashin-tashina acikin al’umma wadda asali an shirya ta ne a matsayin ta lumana.
Adejobi ya kuma ce babu ɗaya daga cikin waɗanda aka kama bisa zalunci, ya na mai cewa sun yi aiki ne da doka yayin gudanar da atisayen kamen.