Za a iya magance cin hanci da rashawa idan kowane ɗan Nijeriya zai bada haɗin kai – Dariye

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon gwaman Jihar Filato, Joshua Dariye, ya bayyana cewa za a iya kawo ƙarshen cin hanci da rashawa a ƙasar nan idan har kowane ɗan Nijeriya zai bayar da haɗin kai.

Sanatan ya bayyana hakan ne a a ranar Litinin, yayin wata hira da gidan talbijin ɗin Channels a shirin NewsNight.

Dariye ya kuma bayyana cewa hukunta shi da aka yi tare da tsohon gwamnan Jihar Taraba, Jolly Nyame, kan aikata rashawa bai kawo ƙarshen sama da faɗi da ake yi kan dukiyar ƙasar ba.

“An ɗaure Dariye da Nyame a magarƙama. Shin ya kawo ƙarshen cin hanci da rashawa? Kamar yadda na faɗa ma mai shari’ana, kana da damar ɗaure ni har na tsawon shekaru 200, idan har hakan zai kawo ƙarshen cin hanci da rashawa, zan yi godiya ga Allah.”

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi wa Dariye, wanda aka hukunta kan sace Naira biliyan 1.16 yayin da yake matsayin gwamnan Jihar Filato daga 1999 zuwa 2007, afuwa a ranar 14 ga watan Afrilun 2022. An yi masa afuwa ne tare da Nyame, wanda aka hukunta shi shi ma kan satar Naira biliyan 1.6.

An kuma sake su daga kurkukun Kuje a ranar 8 ga watan Agustan 2022. Sai dai kuma, Dariye, wanda ya yi godiya ga shugaban ƙasar kan afuwar da ya yi masu, ya ce akwai siyasa a lamarin garƙame shi da aka yi, yana mai cewa wasu sun yi abun da ya fi nasa muni amma aka yafe masu.

Da aka tambaye shi game da yadda za a kawo ƙarshen rashawa a ƙasar, Dariye ya ce: “Idan muna son kawo ƙarshen cin hanci da rashawa, ba abu ne na rana ɗaya ba; za ka ɗauki rashawa don magance rashawa.

Kuma idan ka fara isar da manufofi, bara na baka misali: idan tashar jirgin ƙasa na aiki, ba tare da waɗannan mutane sun yi zagon ƙasa ba, zai rage wahala sosai kan mutanenmu, zai rage farashin kayayyaki, kayan gona.

“Abubuwa ba sa tafiya, wasu mutane da cin gajiyar lamarin, suna wahalar da matakan gwamnati.”

Tsohon sanatan na yankin Filato ta Tsakiya ya kuma bayyana cewa ba zai nemi kowace kujerar gwamnati ba a 2023.