Za a raba wa ‘yan Nijeriya miliyan ɗaya N5,000 kowanen su a tsawon wata 6

Daga UMAR M. GOMBE

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ‘yan Nijeriya miliyan ɗaya da matsalar cutar korona ta shafa za su riƙa karɓar N5,000 a kowane wata har tsawon watanni shida.

Ta ce wannan ya na cikin wani sabon shiri ne da ya fara aiki a farkon wannan shekarar da mutum 3,115 a Legas da Abuja, wanda yanzu za a faɗaɗa shi zuwa sauran dukkan jihohi inda mutane za su fara amfana da shi su ma.

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ta bayyana haka a lokacin wani taron manema labarai da aka yi ran Talata a Abuja inda ta yi ƙarin bayani kan shirin nan na rage raɗaɗin fatara da yunwa a ƙasar nan, wato ‘National Social Investment Programmes’ (NSIP).

A cewar ta, an buɗe rajistar kawo ɗaukin gaggawa (Rapid Response Register, RRR) domin a agaza wa leburori da ke zaune a birane waɗanda matsalolin da annobar korona (COVID-19) ta haifar su ka shafe su kai-tsaye.

Ministar ta ƙara da cewa ana nan an kusa gama tsara kashi na biyu na masu amfana da shirin gwamnati na tallafa wa sana’o’i (wato ‘Government Enterprise and Empowerment Programme’, GEEP) kuma za a sanar kwanan nan.

Ta ce: “Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya ta na kan bakan ta na ci gaba da aiwatar da Shirye-shiryen Haɓaka Rayuwa na Ƙasa, wato ‘National Social Investment Programmes’ (NSIP), bisa ƙudirin Shugaban Ƙasa na tabbatar da cewa an ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga ƙangin fatara da yunwa a cikin shekaru 10, musamman ta sabuwar hanyar sama wa matasa aikin yi da tallafa masu.”

A cewar Hajiya Sadiya Farouq, ma’aikatar ta ta dawo da shirin nan na ciyar da yara ‘yan makaranta (National Home-Grown School Feeding programme), ta ce ɗalibai 9,196,823 ‘yan aji 1 zuwa 3 da ke makarantun firamare na gwamnati kowanne zai karɓi kwanon abinci mai gina jiki a dukkan makarantu 54,619 da ke faɗin ƙasar nan.

Ta ce an faɗaɗa shirin domin ya haɗo da ƙarin yara miliyan 5 bisa umurnin da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayar.

Ministar ta yi kira ga mutane 550,000 da aka ɗauka a kashin ‘batch C’ na shirin N-Power da su garzaya su shiga gidan yanar ‘National Social Investment Management System’ (NASIMS) domin su shigar da bayanan su saboda su samu cancantar ƙarshe ta cin gajiyar tsarin.

Ta ce kashi na biyu da ya ƙunshi wasu ƙarin mutum 500,000 su ma za a ɗauke su nan gaba kaɗan kamar yadda Shugaba Buhari ya umarci a ɗauki mutum miliyan 1 a ƙarƙashin kashin ‘Batch C’.

Ministar ta ce: “Ina kuma farin cikin sanar da ku cewa wannan ma’aikatar ta sake dawo da shirin nan na ciyar da yara ‘yan makaranta (National Home-Grown School Feeding programme)…

“Abin da wannan shiri zai haifar ya haɗa da samun ƙarin yawan yaran da ake ɗauka a makaranta, ƙarin ingantaccen abinci ga yara, haɓaka tattalin arzikin al’ummar wajen da samar da aikin yi ta hanyar aikin masu dafa abinci mutum 103,028, ƙananan manoma 100,000 da sauran masu amfana irin su masu sufurin kaya da za a ɗauka a faɗin ƙasar nan.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *