Za a rage zaman kashe wando idan gwamnati ta taimaki ƙananan masana’antu –Zainab Ali

Daga AMINA YUSUF ALI

Yau filin namu na Kasuwanci ya yi gam-da-katar da wata matashiya wacce ta fara kafa masan’antarta, inda daga rarrafe har ta kai ga babban matsayi, wato Hajiya Zainab Yusuf Ali. Wakiliyar Blueprint Manhaja, Amina Yusuf Ali, ta samu tattaunawa da matashiyar ‘yar kasuwar, inda za ku ji faɗi-tashinta da kuma darussan da za a koya. A sha karatu lafiya. 

MANHAJA: Wacece Hajiya Zainab?
HAJIYA ZAINAB: Da farko dai cikakken sunana shi ne, Zainab Yusuf Ali an haife Ni  a ranar 2 ga Janairun 1985 a Tudun Maliki, Ƙaramar Hukumar Kumbotso. Na yi karatun Firamarena daga 1992-1998 a Bayero University Staff School, na yi karatun Sakandarena a Nana A’isha Girls’ Arabic Secondry School daga 1998-2000. Daga nan aka cire ni aka min aure. Daga nan na samu bayan na yi haihuwar farko 2001 na koma karatu a makarantar matan aure dake Ƙofar Nasarawa, City woman center (laburare) 2001-2004.  Daga nan na tafi Aminu Kano College of Islamic and Legal Studies inda na karanta  daga 2004 – 2007 na yi difiloma, daga nan sai na koma Makarantar Fasaha ta Kano (Kano Polytechnic) ɓangaren HND na fannin Banki da ƙididdiga, daga 2010 zuwa 201. Daga nan na yi Advance diploma wato share fage saboda na canza fannin karatu. Inda na kammala na samu shaidar HND na a shekarar 2015. Sannan na yi bautar qasa a shekarar 2016. Kuma ina da aure da yara shida a yanzu. Kuma ni ce mamallakiya kuma shugabar Kamfanin haɗa kayan kwalliya na Omera Cosmetics production. 

Yaya aka yi kika samu kanki a cikin wannan harka ta haɗa kayan kwalliya?
Ma samu kaina ne a cikin harkar saboda kishin ƙasa. Kullum idan na ga kayayyakin da aka yi a ƙasashen waje sai na dinga jin haushi na ce: “wai me ya sa mu ba za mu yi a ƙasar nan ba?”. Daga nan na fara zuwa wurin masu sinadaran haɗa su man shafawa da sauransu, domin na ga yadda ake yi. Daga nan na fara gwada su basilin, sabulu wanke mota, da sabulu wankin da na wanka da sauransu a shekarar 2012. A 2017 sai Allah ya sa kuma na samu nasarar shiga wata bita ta sati guda da gwamnatin Tarayya ta shirya aƙarƙashin hukumar NDE tdon horaswa a kan haɗa kayan kwalliya. Inda na koyi  abin abubuwa kamar Man wanke kai da na wanka, man shafawa (cream da lotion), turaren ɗaki, da sauransu. Daga nan na fara tunanin fara nawa kamfanin. Inda na fara a shekarar 2018. A halin yanzu ma na yi wa kamfanina na Omera Cosmetics production rajistar NAFDAC, kuma ina haɗa kayayyaki iri-iri masu inganci kamar na waje. Kuma ina samun alkhairi sosai

Ga shi kin yi dogon karatun boko amma me ya sa ba kya yin aikin Gwamnati ko na Banki?
To gaskiya da ma can ni a rayuwata ba na son aiki a ƙarƙashin wani. Na fi so a ce ni ce nake ɗaukar mutane su yi aiki a ƙarƙashinna. To yanzu Alhamdulillah, ina da ma’aikata da dama da suke cin abinci a ƙasana, musamman matan aure. Saboda na tallafa musu kuma na tallafa wa gwamnati na rage yawan masu zaman kashe wando a ƙasar nan. 

Shin Gwamnati ce ta ba ki jari ko kuma ke ce kika haɗa jari ki da kanki?
Na haɗa jarina da kaina. Kuma na fara ne daga dubu biyar da maigidana ya ba ni. Sannan ni ma na haɗa da ɗan abinda nake da shi. Yau da gobe kuma ina juyawa a kasuwanci har jarin nawa ya bunƙasa. Amma kuma akwai jari da hukumar NDE ta ba ni har da bashin banki duk sun tallafa wa bunƙasar jarina. Har na kai matakin da na kai a yanzu. 

Kusan dukkan ‘yan kasuwa suna ƙorafi a kan yadda ‘yan bashi suke ruguza musu kasuwancinsu. Me za ki  ce game da haka?
A gaskiya ni ma ina fama da ‘yan bashi. Musamman mu da muke ba su kaya ba tare sun ba da ko sisi ba. Ko ba komai, don su samu mu tallata kayanmu. Kuma sai sati za su zo su biya kuɗin bayan sun ɗauki kaya ba ko sisi. To idan sati ya zagayo, sai ka ga sun ƙi biyan dukka kuɗin, ko su qi biya gabaɗaya. Wani lokacin ma har su sake roƙar a ƙara musu wani kayan a kan wancan bashin. To amma gaskiya wasu suna biya. Wasu kuwa sai ka ji shiru. To amma yanzu na daina ba da bashi idan ba a biya ba. Sannan yanzu ma na daina ba wa kowa bashi gabaɗaya. A kowacce kasuwa ina da wakili mutum ɗaya. Bayan shi ba na ba wa kowa kayan sai wannan dilan nawa a kasuwar. Shi zai rarraba kaya ga dillalai kuma ya cake min kuɗina cas! Ba sai na ta bin dillalai ‘yan bashi ba. Kuma ba wa mutum guda yana taimakawa ba za a ɓata kasuwa ba. Idan na ba shi shi kaɗai, za ka ga farashin ya tashi bai-ɗaya ba banbanci. 

A halin yanzu kina da diloli nawa, kuma a waɗannan kasuwanni kike da su?
A halin yanzu ina da diloli guda biyar zuwa shida. Biyu a kasuwar Sabon Gari, sai uku a Kasuwar Kurmi, sai a guda ɗaya a Kasuwar Rimi. Da ina da shi a Wambai ma, amma saboda wahalar zirga-zirga, sai na bar kai wa Wambai. 

Hajiya Zainab, kina samun kamar ribar nawa kowanne wata?
(Dariya) Eh to, sirri ne. Amma kowanne wata bayan na sallami ma’aikata da dillalai da kowa, a ƙalla nakan samu ribar dubu ɗari uku ko ma fiye da haka. 
 
Bayan matsalar bashi, wanne ƙalubale kike fuskanta a game da sana’arki a halin yanzu?
Babban ƙalubalen da nake fuskanta shi ne, na hauhawa da rashin tsayayyen farashin kayan aiki da sinadaran haɗa kayana. Kullum farashin kayan aiki yana hawa, su kuma masu saye ba sa ƙaunar su ga an ƙara musu farashi. To ka ga wannan babban ƙalubale ne. Domin sai mun sayi kayan aiki kasuwanci zai tafi. Sannan ƙalubale na biyu, mutanenmu ba su fiye son siyen kayan da aka ƙera na gida Nijeriya ba. Sun fi son siyen na waje duk da wasu kayan namu Alhamdulillah sun fi na wajen ma inganci. Amma saboda mun raina kanmu mun fi ganin darajar kayan wajen. Da za mu dage a kan namu, ba ƙaramin cigaba za mu samu ba a ƙasar nan. Domin gwamnatoci suna zuba maƙudan kuɗaɗe masu yawa wajen shigo da kayayyakin amfani daga waje 

Hajiya Zainab Ali

Zuwa yanzu wanne irin cigaba kika samu?
Alhamdulillah, mun samu cigaba sosai. Domin tun muna rarrafe, yanzu gashi mun miƙe cas, har muna tafiya idan ma ban ce gudu ba. Domin tun muna aiki da hannu mu muttsika, ko mu yi wasu abubuwan. Amma yanzu mun fara amfani da injina a wajen tafiyar da harkokin aikinmu. A yanzu haka na mallaki injinan sabulu na wanka da wanki da sauransu. Sannan muna da kwalaye da ledoji ‘yan kamfani da sunan kamfani mu, da muke zuba kayanmu abin sha’awa. Ba banbanci da kayan waje. 

Meye sirrin nasarar Hajiya Zainab?
(Murmushi) Sirrin nasarar shi e, haƙuri da jajircewa sannan kuma da goyon baya da tallafi daga Mahaifan da maigidana da kuma hukumar samar da aiki ta tarayya (NDE) domin gaskiya a wajensa na samu horo, sannan kuma sun ba ni jari, sannan kuma sun ɗauke ni ina koya wa wasu matan sana’o’ina kuma suna biyana. Don da ba su, da ba na jin na kai matakin da na kai a yau. 

Meye burinki na rayuwa? 
Burkina a rayuwa bai wuce kayanmu da muke ƙerawa a nan ya zamana sun samu karvuwa kamar yadda na waje suka karvu ba. Domin kasuwancinmu zai bunƙasa, kuma za mu ɗauki ƙarin ma’aikata, kuma mu ƙara samar da albashi mai tsoka ga ma’aikatan don mu riƙe su. Hakan zai rage wa gwamnati wahala ta ɗaukar aiki. Wanda yanzu ma aikin babu shi, ba a samu. Sannan kuma gwamnati ta cigaba da tallafa wa masu ƙananan masana’antui kamar namu domin mu ita muke yi wa aiki don mun rage mata masu zaman banza.

Wane kira za ki yi ga mata da masu ƙananan masana’natu?
Kira na gare su shi ne, sana’a irin wannan sai an jure. Rainonta ake kamar jaririya har ta girma. Da haka za a yi ta yi har a gane kan abin. Idan kika yi asara, ba asara ba ce, nasara ce. Domin ƙara miki gogewa take yi. Don za ki kiyaye duk wani kuskure kada ya faru a gaba. Sannan kuma su riƙe aikinsu ba sai sun jira gwamnati ta ba su aikin yi ba. 

Meye saƙonki na ƙarshe?
Saƙona na ƙarshe shine godiya ta musamman ga mahaifina, Sheikh Dakta Yusuf Ali, da mijina, Alhaji Sani Yau Ɓaɓura, kan ba ni dama da goyon baya da ƙarfafa min gwiwa da suka yi, domin ba ya nuna fushinsa a kan duk wasu harkoki na ayyukana. Sannan Ina godiya ga hukumar NDA kan tallafi da suka yi min. 

To Hajiya Zainab, mun gode. 
Ni ma na gode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *