Za a rataye ɗan shekara 22 saboda fashi da makami a Ekiti

Daga WAKILINMU

Babbar Kotun jihar Ekiti mai zamanta a Ado-Ekiti, ta yanke wa wani matashi ɗan shekara 22 mai suna Kehinde Olajide hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda aikata laifin fashi da makami.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kotun ta saki wasu ‘yan gida ɗaya da aka alaƙanta su da fashin, wato Kareem Azeez mai shekara 24 da Bamisile Lateef ɗan shekara 28 da kuma Adebayo Basiru ɗan shekara 25.

Yayin da yake yanke hukuncin ran Alhamis da ta gabata, Mai Shari’a Lekan Ogunmoye, ya ce masu gabatar fa ƙara sun gabatar da gamsassun hujjojin aikata fashi da makami a kan mai laifi na farko ba tare da wata shakka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *